Man United ta sanar da yin hasarar £6.9m

Asalin hoton, Getty Images
Rashin halartar Champions League a bana da biyan kuɗin da ya shafi rage ma'aikata ya sa Manchester United ta yi hasarar £6.9m a zangon farkon 2024/25.
United ta kare a mataki na takwas a bara karkashin Erik ten Hag, wanda aka kora cikin Oktoba - gurbi mafi muni da ta yi a Premier, hakan ya sa ba ta samu shiga Champions League ba.
Hakan ya sa ta kasa a samun kuɗin shiga a fannin watsa shirye-shiryenta da kaso 20.4 cikin 100, wato £31.3m daga 30 ga watan Satumba.
To sai dai bayan da United ta lashe FA Cup a bara, hakan ya sa ta samu gurbin Europa League.
Haka kuma United ta yi hasarar kasuwancin da ya kai kaso 5.6 cikin 100 a zangon farko daga £90.4m ya koma £85.3m.
United ta samu raguwa a fannin kallon wasanninta a sitadiya daga kaso 3.3 cikin 100 daga £27.4m ya koma £26.5m.
A baya ƙungiyar Old Trafford ta ce dalilin sauye-sauyen da ta gudanar a bara, tana sa ran za ta samu rarar kuɗi tsakanin £40m zuwa £45m, wanda zai iya yin tasiri a kasuwancin 2025 zuwa ta 2026.
United ta sanar da cin ribar £1.9m a irin wannan zangon a bara, amma sai ta sanar da asarar da ta kai £113.2m.
Haka kuma ƙungiyar ta ce ta samu ragi wajen biyan albashi da ya kai £10.1m daga £80.2m, hakan ya biyo bayan canje-canjen da ta yi wajen biyan ƴan wasa.












