Alexander-Arnold na dab da zuwa Madrid, Man Utd za ta sayar da ƴanwasa 10

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗanwasan Liverpool da Ingila Trent Alexander-Arnold, mai shekara 26, ya aminta ya ƙulla yarjejeniyar shekara biyar da Real Madrid. (Sky Sports Switzerland - in French)

Real kuma na ci gaba da farautar ɗanwasan Athletic Bilbao da Spain Nico Williams, wanda farashinsa ya kai sama da fam miliyan 51 idan har Vinicius Jr, mai shekara 24, ya yanke shawarar komawa Saudiyya. (Fichajes - in Spanish)

Manchester United na shirin raba gari da ƴanwasa kusan 10 da suka haɗa da Marcus Rashford, mai shekara 27 da ɗanwasan tsakiya na Brazil mai shekara 33 Casemiro. (Manchester Evening News)

United kuma na son ɗauko ɗanwasan Fenerbahce Yusuf Akcicek, mai shekara 19, duk da Tottenham Hotspur da Bayern Munich da Atletico Madrid da Napoli da RB Leipzig na farautar ɗanwasan na Turkiya. (Mirror)

Barcelona na son ɗauko ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Italiya Sandro Tonali, mai shekara 24, da kuma abokin wasansa na Sweden Alexander Isak, mai shekara 25. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Ɗanwasan tsakiya na Barcelona da Netherlands Frenkie de Jong na son ci gaba da taka leda a ƙungiyar yayin da yake tattaunawa kan sabunta kwangilar shi. (NY Times - subscription required)

Ɗanwasan baya na Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 22, na nazarin makomarsa a Everton yayin da Manchester United da Liverpool suka nuna sha'awarsa. (Mirro, externalr)

Tottenham Hotspur ta taya ɗanwasan tsakiya na Sunderland Chris Rigg kan fam miliyan 37. (Fichajes - in Spanish)

Ɗanwasan tsakiya na Brazil Andrey Santos ba ya da tabbas kan makomar shi a Chelsea duk da yana son sake taka leda da Estevao Willian bayan zuwa aro a Strasbourg. Willian, mai shekara 17 zai dawo taka leda a Chelsea Yuli daga Palmeiras. (Evening Standard)