Hare-haren Lebanon: Yadda masu aikin ceto ke sadaukar da rayuwarsu

    • Marubuci, Rami Ruhayem
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent
    • Aiko rahoto daga, Beirut
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Rundunar sojin Isra'ila ta yi ta kai wa tawagogin ceto da agaji, da cibiyoyin lafiya, da asibitoci hari a faɗin Lebanon tun bayan fara ƙaddamar da yaƙi kan ƙungiyar Hezbollah a watan da ya gabata.

Hare-haren sun kashe tare da raunata gomman ma'aikatan lafiya da masu aikin ceto, abin da ya sa ta yanke kudancin ƙasar daga samun wasu muhimman ayyukan agajin gaggawa.

Akwai ƙungiya ɗaya da lamarin ya fi shafa sama da kowa. Islamic Health Society (IHS), wadda Hezbollah ke ɗaukar nauyi, kan gudanar da ayyuka a asibitoci da cibiyoyin lafiya a faɗin ƙasar.

Zuwa ranar Juma'a, an kashe ma'aikatanta sama da 85 tare da raunata fiye da 150, a cewar Bilal Assaf, shugaban sashen hulɗa na IHS Civil Defense.

Da tsakar dare a ranar 7 ga watan Oktoba, Isra'ila ta kai wa cibiyar aikin agaji a Baraachit hari a Bint Jbeil da ke kudancin ƙasar, inda ta kashe aƙalla ma'aikatan kashe gobara 10, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta bayyana.

Ma'aikatan IHS na ta ƙoƙari a yankin saboda wasu mazauna da suka ƙi barin gidajensu, amma dakarun Isra'ila ba su bar su sun gudanar da ayyukansu ba.

"Duk lokacin da suka fita, sai an kai hari kusa da motocinsu," in ji Assaf.

A wata safiyar Litinin, harin Isra'ila ya lalata wani gini da suke zaune.

Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce harin "kisan gilla" ne.

'Yan awanni bayan harin, ƙungiyar Red Cross ta Lebanon ta isa wurin kuma ta tarar da gawar mutum takwas.

Akwai wasu da yawa a ƙarƙashin ɓaraguzai, amma ba za su iya ceto su ba saboda tawagar ceton ba za ta iya kaiwa gare su ba, a cewar Assaf.

Kwanaki bayan harin kuma, har yanzu akwai wasu ma'aikatan kashe gobara da ke ƙarƙashin ɓaraguzan.

Yayin da Lebanon ke fama da yawan mutanen da ke rasa muhallansu, sakamakon hare-haren Isra'ila a wasu sassan ƙasar, ƙungiyar agaji ta IHS da wasu masu aikin sa kai da hukumomin gwamnati da sauran ƙungiyoyi na ci gaba da bayar da agaji ga mutanen da hare-haren ke shafa.

Wata makaranta daga cikin makarantu da dama a birnin Beirut - da suka zama tattarar ɗaruruwan mutanen da suka guje wa hare-haren Isra'ila a kudancin birnin Beirut - ta zama tamkar gida ga mutanen.

Mutanen sun shanya riguna da sauran tufafi a tagogin azuzuwan, ga wasu yara nan na wasa a filin makarantar, wasu da bal wasu kuma kekuna.

Wasu daga cikin matasan da ke makarantar sun taru a kan kyamararmu, suna bayyana ƙorafinsu kan ƙarancin ruwan sha a wurin.

'Kowa a cikinmu ya san wani da ya yi shahada'

Ali Freidi, wanda ke kula da cibiyoyin lafiya na ƙungiyar agaji ta IHS, ya bayyana mana cewa sun sanya likitoci da ma'aikatan jinya da masu bayar da shawarwari kan lafiyar ƙwaƙwalwa, domin taimaka wa dubban mutanen da aka raba da muhallansu.

Ya amince da matsin lamba da IHS ke sha, sakamakon ƙaruwar buƙatocin mutanen da suka rasa muhallansu, da kuma hare-haren Isra'ila kan takwarorinsu ma'aikatan agaji.

“Mu wani ɓangare ne na al'umma,” in ji shi. “kowa a cikinmu ya san wani da ya yi shahada.”

Batoul Hammoud, mai shekara 25, malamar makaranta ce kuma mai aikin bayar da agaji tare da ƙungiyar IHS.

Ta ce ita da sauran takwarorinta masu aikin sa kai sun yi ta zagaya makarantar da take koyarwa da kuma wata makarantar a yankin, domin ganin yadda za su tallafa.

“Babban abin da ake buƙata shi ne magani. Mutane da dama sun tsere daga gidajensu ba tare da sun ɗauki maganinus ba''.

Ƙungiyar IHS na gudanar da ayyukansu na yau da kullum, kamar lura da hawan jinin tsofaffi daga cikin mutanen da suka rasa muhallansu, kamar yadda ta bayyana.

“A matsayina na malamar makaranta, ina kuma kwantar wa ƙananan yara hankali, wajen shirya musu wasu abubuwan kwantar da hankali, a wasu lokutanma mukan ce musu su riƙa kwantar da hankulansu''.

An kafa ƙungiyar bayar da agaji ta IHS ne a shekarun 1980 lokacin da ake tsaka da yaƙin basasa, da mamayar Isra'ila a kudanci da kuma yunkurin ɓallewar ƙasa a Lebanon.

Daga baya kuma gwamnati ta bai wa ƙungiyar lasisi, inda yanzu kuma take aiki tare da hukumar lafiyar ƙasar.

Ta kuma ƙulla yarjejeniyoyi da wasu jihohin ƙasar wajen gudanar da cibiyoyin lafiya da ayyukan jin ƙai.

Yayin da ma'aikatan lafiya ke cikin matsin lamba a faɗin ƙasar, ƙungiyar ta fuskanci casgaro da dama fiye da kowace ƙungiyar lafiya.

A ranar 3 ga watan Oktoba, Isra'ila ta kai hari kan cibiyar ƙungiyar da ke tsakiyar birnin Beirut, tare da kashe mutum tara da jikkata 14.

Mafi yawancin waɗanda suka mutu masu tsaron fararen hula ne, da ma'aikatan lafiya waɗanda ba su jima da kammala aikin ceto a wani wuri a kudancin ƙasar, inda aka samu manyan hare-haren boma-boman Isra'ila.

Kashe gari kuma aka kashe wasu ma'aikatan lafiya bakwai a wani hari da Isra'ila ta kai kan motocin ɗaukar marasa lafiya na IHS a kusa da mashigar asibitin Marjaiyoun a kudncin ƙasar. A ranar ne kuma asibitin ya dakatar da ayyukansa.

Haka kuma a wannan ranar ne dakarun Isra'ila suka kai hari kan asibitin Ghandour da ke Bint Jbeil, wanda ƙungiyar IHS ke gudanarwa, inda aka raunata likitoci da dama da ma'aikatan asibitin.

Shi ma asibitin ya dakatar da ayyukansa bayan wannan harin.

Daraktan asibitin, Dakta Mohammad Sleiman ya shaida mana cewa asibitin na aiki da kyau har zuwa wannan rana, duk da yaƙin da ke gudana a kewayensa.

“Muna da magunguna da kayan aiki. Shirin gwamnati na tafiya yadda ya kamata, ba mu da wata matsala a wannan rana. Amma muna neman kariya,'' in ji shi.

'Waye ba zai so irin wannan aiki a cikinmu ba?'

Sojojin Isra'ila sun fitar da jerin sanarwa da acikin suke zargin ƙungiyar Hezbollah da amfani da motocin ɗaukar marasa lafiya wajen jigilar mayaƙa da makamanta.

Isra'ilar ta kuma bayyana kai har cibiyar bayar da agaji da Baarachit sakamakon ''samun gamsassun bayanan sirri kan yadda mayaƙan Hezbollah ke amfani da cibiyar a matsayin sansanin sojinta a lokacin yaƙin''.

Haka kuma ta zargi Hezbollah ta ''cutar da fararen hula ta hanyar amfani da wurarensu''.

Ta kuma ce harin da ta kai cibiyar IHS a tsakiyarBeirut ta yi ne da niyyar ''lalata kayayyakin 'yan ta'adda''.

Bayan harin kan cibiyar lafiya a tsakiyar Beirut, shugaban manufofin waje na ƙungiyar EU ya ce ''Ba fararen hula ne kaɗai hare-haren ke shafa ba, har da cibiyoyin bayar da agaji, inda ya yi Allah wadai da matakin da ya kira ''saɓa wa dokokin duniya.

Kakakin ƙungiyar bayar da agajin ta IHS, Mr Assaf, ya ce ƙungiyar ba ta da alaƙa da aikin soji sanna ta zargi Isra'ila da kai hare-hare kan cibiyoyin bayar da agajin gaggawa a yankunan da take son tilasta wa fararen hula ficewa.

“A mako biyu da suka gabata a kwai mutane da ke zaune a cibiyar Bint Jbeil,” in ji shi.

“Kasancewarmu a wurin ya samar musu nutsuwa, mutanenmu sun riƙa samar musu abinci tare da kula da su''.

A ranar Juma'a, Majalisar Dinikin duniya ta ce fiye da ma'aikatan lafiya 100 aka kashe a Lebanon tun bayan fara rikici tsakanin Isra'ila da Hezbollah kusan shekara guda da ta gabata.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce tun ranar 17 ga watan Satumba, an kai hare-hare 18 kan cibiyoyin lafiya a Leabon, tare da kashe ma'aikatan lafiya 72.