Shugaba Biden ya yi watsi da buƙatar kama Firaministan Isra'ila

An wallafa

Shugaba Biden ya sake jaddada matsayar sa ta kare Isra’ila, sa’oi kaɗan bayan mai gabatar da ƙara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya ce ya nemi a bashi isinin kama Benjamin Netanyahu da kuma ministan tsaron sa, a bisa zargin aikata mummunan manyan lafuka a Gaza.

Da yake tsokaci a kan shari’ar da aka yi mataki-mataki a kotun ta duniya, Mr Biden ya haƙiƙance cewa dakarun Isra’ila ba su aikata kisan gilla a Gaza ba.

Da yake jawabi a fadar White House, lokacin wani tarom yahudawa, Mr Biden ya ce ko kusa babu-haɗi a tsakanin Isra’ila da Hamas.

Manyan saanatocin Amurka ma, daga democrat da kuma republica sun Allah wadai da matsayar mai gabatar da ƙarar na kotun duniya, kuma ɗan republican Mitch McConnell ya buƙaci ƙasashen Yamma su ɗauki ƙwararan matakai a kan kotun.

Ya ce: “A yau ma wata sabuwa ta ɓulla a kafafen yaɗa labarai. Lokaci ya yi da shugaban ƙasa da kuma shugabannin Turai su ɗauki matakin da ya dace.

Ku goyi bayan ƴancin Isra’ila na kare kanta daga hare-haren manyan ƴan ta’adda irin su Sinwar, ku kuma yi turjiya ga almarar da kotun birnin Hague ke fitarwa game da ƙasar da bata da alaƙa da ita, ku kuma mayar da hankali wajen ɗaukar tsauraran matakai a kan kotun da maƙarraban ta, idan har suka aikwatar da mummunan muradin su a kan Isra’ila..”

Tun da farko dai, Firaiministan Isra'ila Banjamin Netanyahu ya yi Allah-wadai da bukatar mai gabatar da kara na Kotun Duniya ta neman a kama shi da wasu shugabannin Hamas bisa zargin aikata laifukan yaki a Gaza.

Mai gabatar da karar ICC Karim Khan ya ce akwai kwararan hujjoji kan cewa Netanyahu da Ministan tsaron kasar sun aikata laifukan yaki a Gaza.

Babban mai gabatar da ƙarar ya gabatar da hujjojin da aka tattaro a Gaza ga alkalan kotun.

Yanzu hankali ya koma kan alkalan, domin ganin ko za su ba da izinin kama shugabannin nan da makonni masu zuwa.