Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka ta tabbatar da isar kayan agaji Gaza ta ruwa
Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da isar kashin farko na kayan agaji zuwa dandamalin da aka gina a gabar teku da ke zirin Gaza.
Wannan dai na ɗauke ne a wani saƙo da suka wallafa a shafinsu na X, inda sanarwar ta ce manyan motoci ɗauke da kayan agaji sun fara tafiya a kan dandamalin da Amurka ta gina da misalin ƙarfe 0900 agogon Amurka.
"Wannan aiki na tafiya, hoɓɓasar ƙasashen duniya na kai ƙarin kayan agaji ga al'ummar Falasɗinawa a Gaza ta hanyar ruwa ," kamar yadda sanarwar ta ce.
Amurka ta fara gina gadar ruwan ne 'yan makonni da suka gabata domin taimakawa wajen kai wa al'ummar Gaza agaji, a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da yaƙar ƙungiyar Hamas.
Vice Adm Brad Cooper, wanda mataimakin kwamandan cibiyar tsaro ta Amurka ne, ya ce jirage za su ɗauko kayan daga Cyprus domin kai su zuwa dandamalin da ke da ke gabar kogin Gaza.
Ƙananan jiragen ruwa na Amurka ne za su ɗauki manyan motoci 15 na dakon kaya sai daga bisani su motocin su ɗebi kayan zuwa dandamalin wanda yake da tsawon ɗaruruwan mita da ke haɗe bakin ruwa.
Manyan motoci za su yi tafiya a kan dandamalin kafin ajiye agajin a wani wuri a bakin ruwan.
Hukumomi sun ce hukumar da ke kula da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ita ce mai alhakin rarraba kayan agajin.