Na tarar da yanayi marar kyau a Man Utd - Erik ten Hag

An wallafa

Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce ya gaji yanayi marar kyau a Old Trafford yayin da kuma ya ki yin ƙarin haske kan makomar Jadon Sancho.

Wannan na zuwa bayan Jadon Sancho ya yi atisaye shi kaɗai ba tare da tawagar Manchester ba har sai ya sasanta da kocin.

Kocin ya ajiye Sancho a benci a wasan da Arsenal ta doke Manchester United 3-1 saboda a cewar kocin rashin nuna ƙwazo wajen atisaye.

Kocin ya ce an kawo shi Old Trafford ne domin tabbatar da sauyi, yana mai cewa, "ba aikina ba ne na daidaita abubuwa," in ji Ten Hag.

Ya samu yabo wajen tabbatar da ɗa'a a Old Trafford musamman yadda ya ajiye Cristiano Ronaldo da Marcus Rashford a benci a kakar da ta gabata.

Baya ga Sancho, Manchester na fama da matsaloli na ƴan wasa saboda rauni musamman Raphael Varane da Luke Shaw da Mason Mount.

Kodayake, Lisandro Martinez da Victor Lindelof ana tunanin sun murmure.