Osimhen na jiran Arsenal, Bayern Munich na zawarcin Fernandez

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 25, yana jiran tayin Arsenal ko kuma daga wata ƙungiya a Saudiyya. (Gazzetta dello Sport)
Bayern Munich ta fara zawarcin ɗan wasan tsakiyar Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 29, daga Manchester United. (Ya Jogo)
Jadon Sancho, mai shekara 24, a shirye yake ya koma United idan zaman aronsa ya kare a Borussia Dortmund - amma sai idan Erik Ten Hag ya bar ƙungiyar a bazara. (Mirror)
Tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya gana da daraktan wasanni na Crystal Palace Dougie Freedman a birnin Landan domin nazarin matsayinsu kan yiwuwar sayar da ɗan wasan bayan Ingila Marc Guehi mai shekaru 23 da dan wasan tsakiya na Ingila Eberechi Eze mai shekaru 25 da kuma dan wasan Faransa na ƴan ƙasa da shekara 21 Michael Olisemai shekaru 22, a wannan bazarar. (Football Insider)
Palace za ta koma kan dan wasan Leeds dan ƙasar Holland Crysencio Summerville, mai shekara 22, idan ta sayar da Olise ko Eze a wannan bazarar. (Mirror)
Ana sa ran ɗan wasan Belgium Kevin de Bruyne, wanda zai cika shekaru 33 a ƙarshen wannan watan, zai samu tayin barin Manchester City a wannan bazarar. (Football Insider)
Cristiano Ronaldo ya tattauna da wasu tsoffin abokan wasansa guda biyu a wani yunƙuri na shawo kansu don su kasance tare da shi a Al Nassr - ɗan wasan baya na Real Madrid Nacho Fernandez, mai shekara 34, da kuma ɗan wasan tsakiya na Manchester United da Brazil Casemiro, mai shekara 32. (Marca).
A ranar Litinin ne za a sanar da kocin Leicester City Enzo Maresca a matsayin sabon kocin Chelsea, bayan da ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyar. (Fabrizio Romano)
Newcastle United za ta yi ƙoƙarin kammala cinikin ɗan wasan Bournemouth da Ingila Lloyd Kelly, mai shekara 25, a wannan makon. (Telegraph)
Ana sa ran bayyana tsohon kocin Chelsea da Tottenham Antonio Conte a matsayin sabon kocin Napoli a wannan makon. (Nicolo Schira)











