'Yan Real Madrid da suka ziyarci Celta a gasar La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta ziyarci Celta Vigo, domin buga wasa na biyu a gasar La Liga ta bana da za su fafata ranar Asabar.
Wasa na biyu a jere kenan da Real za ta yi a waje, bayan makon farko da ta ziyarci sabuwar kungiya Almerira.
Real ce ta yi nasara da ci 2-1 a wasan farko da ta yi ranar 14 ga watan Agusta, inda Almeria ta fara cin kwallo ta hannun Largie Ramazani.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Real ta farke ta hannun Lucas Vazquez, sannan David Alaba ya kara na biyu da ya bai wa Real maki ukun da take bukata.
Real ce ta lashe La Liga a kakar da ta wuce na 35 jumulla, sannan ta dauki Uefa Super Cup a bana, bayan doke Eintranch Frankfurt.
Kociyan Real, Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da ya je da su karawa da a filin wasa na Balaidos. 'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Luis López.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Rüdiger da F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Modrić, Camavinga, Valverde, Lucas V., Tchouameni da D. Ceballos.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr. da Mariano.









