Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
AL-Ettifaq ta yi lattin taya Sancho Arsenal za ta sayar da Pepe
Al-Ettifaq ta yi lattin taya dan wasan Manchester United, Jadon Sancho, bayan da aka rufe kasuwar saye da sayar da ' yan kwallo ranar Alhamis, wadda ta so daukar aron dan wasan tawagar Ingila mai shekara 23. (CBS Sports)
Al-Ettifaq ta kasa daukar Sancho na Manchester United wadda ta bukaci fam miliyan 50 cikin yarjejeniyar sayen dan wasan. (Mail)
Tsohon kocin, Brighton da Chelsea Graham Potter, mai shekara 48, ya yi watsi da damar maye gurbin Laurent Blanc a Lyon mai buga Ligue 1. (90 Min)
Lyon na son zawarcin tsohon kocin Wolves da tawagar Sifaniya, Julen Lopetegui, ko mai horar da Lille Paulo Fonseca domin damka masa ragamar kocin kungiyar. (Sky Sports)
Watakila tsohon dan kwallon tawagar Ingila, Wayne Rooney, mai shekara 37, ya maye gurbin John Eustace idan ya bar Birmingham City, wanda ake alakanta shi da kociya, Swansea ko kuma Rangers. (Telegraph - subscription required)
Arsenal na fatan sayar da dan kwallon Ivory Coast, Nicolas Pepe ga Besiktas ko Trabzonsp, wadanda keda sha'awar daukar dan wasan mai shekara 28. (Evening Standard)
Chelsea ta yi wa Brugge tayin dan wasan gefenta na kasar Norway Antonio Nusa akan fam miliyan 23 sai dai kungiyar kwallon kafa ta yi watsi da tayin a ranar da wa'adin cikin 'yan wasan kwallon kafa ya zo karshe.( Evening Standard)
Anki sallama tayin da Chelsea ta yiwa Antonio Nusa fam miliyan 23 na Club Brugge, za kuma ta fuskanci kalubale nan gaba, bayan da manyan kungiyoyin Turai a kalla su 20 da ke bibiyar dan wasan mai shekara 18. (Evening Standard)
Dan kwallon Ingila, Jesse Lingard, mai shekara 30, zai buga wa West Ham wasan sada zumunta da Ipswich ba 'yan kallo, yayin da West Ham za ta yi bazarin ko ya dace ta bai wa tsohon dan wasan Manchester United. (Mail)
Eja din dan wasan Napoli, Kvicha Kvaratskhelia ya ce dan kwallon mai shekara 22 na jin dadin zama a kungiyar da ke buga Serie A, kuma ba su taba tattaunawa ba kan barin Napoli ba. (CalcioNapoli24, via Football Italia)
Fulham na tattaunawa wa da Harrison Reed kan tsawaita yarjejeniyar, bayan da aka ki sallama tayin fam milyan uku da Wolves ta yi wa dan wasan mai shekara 28. (Evening Standard)
Bournemouth ta yi watsi da tayin fam miliyan 20 da aka yiwa mai tsaron baya, Lloyd Kelly a bana, kuma Tottenham da Liverpool da Newcastle za suyi rige-rigen sayen dan kwallon mai shekara 24 a watan Janairu. (90 Min)