Liverpool ta ga samu ta ga rashi a Everton a Premier

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Everton da Liverpool sun tashi 2-2 a a kwantan wasan Premier League a Goodison Park ranar Laraba.

Mai masaukin baƙi ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Beto a minti na 11 da fara wasan, sai dai minti biyar tsakani Liverpool ta farke ta hannun Mac Allister.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Liverpool ta kara na biyu ta hannun Mohamed Salah, daf da za a tashi Everton ta farke ta hannun Tarkowski.

An bai wa Curtis Jones na Liverpool jan kati, sakamakon da ya je ya ture Abdoulaye Doucoure, wanda ke murnar tashi 2-2 a gaban magoya bayan ƙungiyar Anfield.

Shima Doucoure ya karɓi jan katin, bayan da suka fara faɗa a tsakaninsu, duk da an tashi daga fafatawar a lokacin da lamarin ya faru.

Karo na 122 da suka kece raini a tsakaninsu a wasan na hamayya da ake kira Mersyside Derby a gidan Everton.

Wannan shi ne wasan karshe da suka buga a gidan Everton, wadda za ta koma Bramley-Moore Dock a karshen kakar nan, bayan da take Goodison Park tun 1892.

Tun farko an tsara buga wasan ranar 7 ga watan Disambar 2024, amma sai aka soke karawar, sakamakon gagarumar guguwa da mamakon zubar ruwan sama.

Tun bayan da David Moyes ya sake karbar aikin horar da Everton daga ranar 11 ga watan Janairu, ya yi wasa shida da yin nasara uku da canjaras ɗaya aka doke shi wasa biyu.

Da wannan sakamakon Liverpool ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburin Premier League da maki 57 da tazarar maki bakwai tsakani da Arsenal ta biyu.

Ita kuwa Everton, wadda ta haɗa maki 27 ta yi sama zuwa mataki na 15 a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.

Ranar Lahadi 16 ga watan Fabrairu Liverpool za ta kara da Wolverhampton a wasan mako na 25 a Premier League.

Everton kuwa za ta je Crystal Palace ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu, a kuma ranar ce Leicester City za ta karɓi bakuncin Arsenal.