Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasar da mata ke fama da matsalar fyaɗe
- Marubuci, Geeta Pandey and Seetu Tiwari
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News & BBC Hindi
- Aiko rahoto daga, Delhi & Begusarai
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Shekara 13 bayan fyaɗen da aka yi wa wata mata ƴar Indiya a cikin motar bas a babban birnin ƙasar Delhi ya ɗauki hankalin duniya, wani sabon lamari da ya kusa kama da irin wancan cin zarafin matan ya sake faruwa a jihar Bihar da ke arewacin kasar.
Masu fafutuka sun ce labarinta shi ma manuniya ce kan rashin kulawa da matan da aka ci zarafi ke fama da shi a hannun ƴansanda da hukumomin kiwon lafiya, musamman a garuruwa da ƙauyuka a Indiya.
Gargaɗi: Wasu bayanan da matar ta shaidawa BBC na da ban tsoro da tayar da hankali.
Dokar Indiya ta hana bayyana sunayen waɗanda aka ci zarafinsu ta hanyar lalata, don haka za mu kira wannan mata da suna Soma (ba ainihin sunanta ba).
Mai shekara 28 kuma uwar ƴaƴa huɗu ta shaidawa sashin Hindi na BBC cewa an kai mata hari ne har cikin gidanta, kuma wasu gungun mutane suka yi mata fyaɗe tare da cusa mata wasu abubuwa a farjinta.
Lamarin ya faru ne a cikin dare a ranar 11 ga watan Yuni, a Begusarai, wani yanki da aka yarda a hukumance cewa yana cikin mafi koma baya a faɗin Indiya.
Abin da aka yi mata ya ɗauki hankali a ƙasar bayan hukumomin asibiti sun bayar da tabbacin cewa sun ciro wasu abubuwa da aka cusa mata a farjinta bayan an yi mata fyade. Kuma matar ta gabatar da wani akwakun sanya harsashi, wanda ta ce yana daga cikin abubuwan da aka cusa mata.
A labarin da ta bayar kan mummunan cin zarafin da aka yi mata, Soma ta ce tana cikin bayi a gidanta mai ɗaki ɗaya tilo da dare, sai wasu maza biyar suka kutsa cikin gidan. Bayin gidan bashi da ƙofa sai dai wani labule da aka rataya domin rufe tsiraici.
Ta ce "Sun kama ni, suka ɗaure hannuwa na. Da na yi yunƙuri guduwa sai suka yanke ni da reza a ƙirjina sannan suka yi mani fyaɗe,''
Ta ce da farko mijinta ya ɗauka mage ce take kuka, a lokacin da ya ji motsi, amma daga baya da abin ya yi yawa sai ya tashi domin duba abin da ke faruwa.
"Amma sun kulle gidan ta baya. Sai ya kira wani maƙwabcinmu wanda ya buɗe ƙofar suka fito kuma kowa ya ga halin da nake ciki sai kawai ya fashe da kuka.''
Babbab jami'in ƴansandan Begusarai, Maneesh (wanda ke amfani da suna ɗaya tilo) ya shaidawa BBC cewa rahoton da likitoci suka bayar bayan kammala gwaji a kan Soma ya tabbatar da cewa an yi mata fyaɗe.
Ƴansanda sun ce wasu daga waɗanda ake zargi da aka kama suna da tarihin aikata manyan laifuka kuma ikin su harda waɗanda aka taɓa kamawa da aikata fyaɗe.
A ranar da mummunan al'amarin ya faru, Soma ta ce ba ta samu kulawar da ya kamata ba a wajen ƴansanda da kuma hukumomin lafiya.
Mijinta, wanda ke tuƙa a daidaita sahu (Keke Napep) ya ɗauki matar tashi zuwa wani ofishin ƴansanda mai nisan kilomita uku daga gidansu. Ya ce ƴansanda suka ƙi ɗaukar bayanan su, a madadin haka sai suka shawarce shi da ya kai ta wajen likita.
Tuni aka dakatar da babban jami'in ƴansandan saboda ''sakaci da aiki da wariya da rashin tausayi'', kamar yadda ƴansandan Begusarai suka ce. Sun ce an fara shigar da ƙorafi game da batun ne a ranar 13 ga watan Yuni.
Tun bayan fyaɗen, Soma da mijinta sun ce ta yi ta fama don neman samun kulawar kiwon lafiya da take buƙata.
A ranar da aka kai mata hari ma, rahotanni sun ce wata cibiyar kula da lafiya matakin farko ta ƙi karɓar ta, saboda wai ba su karɓar masu buƙatar kulawar gaggawa kuma basu da likita a ƙasa. Sai aka kai ta wata cibiyar kiwon lafiya ta gwamnati da ke yankin, inda aka ba ta kulawar gaggawa sannan aka tura ta zuwa babban asibiti.
Soma ta shaidwa BBC cewa kulawar da ta samu a asibitin ba ta wadatar ba.
Baya ta dawo hayyacin ta a ranar 12 ga watan Yuni, ta faɗa wa mijinta yadda likita ta riƙa zolayarta da maganar fyaɗen. "Da take mani allura, likita ta riƙa damuna da tambaya 'ke ma an yi maki fyaɗe ne?' ina ta amsawa amma sai ƙara tambaya ta ke,'' in ji Soma.
Ashok Kumar, babban likita a asibitin Begusarai, ya shaidawa BBC cewa an kawo matar ne a bisa ƙorafin cikin ta na ciwo. Kuma sai a ranar 13 ga watan Yuni aka sanar da su cewa fyaɗe aka yi mata, kuma nan da nan aka yi mata duk wani gwaji da ake buƙata.
An sallami Soma, amma kwana ɗaya kacal ta yi a gida aka ƙara mayar da ita bayan ta suma. Mijinta ya shaidawa BBC cewa ko da suka koma asibitin, kwana ɗaya kacal ta sake yi aka sallame ta.
Mijin ya ce "Wata angwanzoma da ta duba ta a gida ce ta gano cewa akwai wani abu a cikin farjinta saboda tana ta suma tana farfaɗowa. A ranar 18 ga watan Yuni ta nuna mana wani akwakun harsashi da ya faɗo daga cikin farjinta,'' Ya ƙara da cewa daga nan suka mayar da ita asibiti.
"Kwakon harsashi ne da babu komai a ciki,'' inji Kumar. "Muna ƙara duba ta, kuma an ciro wasu abubuwan daga cikin ta. Yanzu dai tana murmurewa.''
Abin daya faru da Soma ya janyo hankalin ƴan Indiya kuma an riƙa kwatanta shi da irin wanda akayi wa wata ɗalubamaishekara 23 a Delhi wadda itama aka cusa mata abubuwa a farji, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuar ta.
Wannan laifin ya janyo suka da Allah wadai daga sassan duniya da zanga-zanga a Indiya kuma ya sanya a ɓullo da sabbin dokoki masu tsauri kan laifin fyaɗe, ciki harda hukuncin kisa. Wasu maza huɗu da aka kama da laifi kuma kotu ta yanke masu hukunci a 2020 sun fuskanci tsattsauran hukunci inda har ɗaya daga cikin su ya mutu a gidan yari.
Amma duk da tsauraran matakan hukuni da aje ɗauka, ana samun rahoton fyaɗe har guda 30,000 a Indiya kowacce shekara.
Can a Begusarai, Soma na ci gaba da jinya a asibiti amma ana yawan damun ta da ziyara daga ƴanjarida da ƴansiyasa da kuma ƙungiyoyin fararen hula. Har yanzu tana cikin azaba amma tana fatan komawa gidanta bayan a warke.
Ta ce "Ina cikin damuwa saboda na ƙosa in koma gida ga ƴaƴana, ƙananan yara ne kuma a yanzu ana riƙon su ne wajen ƴan uwana da ke zama a wani ƙauye mai nisan kilomita 35 daga nan. Na ƙosa in koma gida don ci gaba da rayuwa tare da su.''