Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/06/2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Duk wani katsalandan ga ikon ƙasarmu a mashigar Hormuz zai ƙara tsananta rikici ne - Iran

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na katsalandan a yadda Iran ke tafiyar da mashigar Hormuz zai ƙara tsananta rikici a yankin.

    Araqchi, wanda ke ziyara a birnin Baghdad, ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai tare da takwaransa na Iraq, inda ya ce bisa fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka, za a dawo da zirga-zirgar mashigar cikin kwanaki 30, a ƙarƙashin cikakken ikon Iran kaɗai.

    Ya jaddada cewa Iran ce ke da alhakin aiwatar da wannan tsari, yana mai cewa duk wani ƙoƙari na ƙirƙirar wata hanya dabam ko tsoma baki daga waje zai janyo tsaiko da kuma ƙarin rikice-rikice, wanda a cewarsa tuni an fara gani a abubuwan da suka faru cikin dare biyu a yankin.

    A cikin kwanaki uku da suka gabata, an kai hari kan aƙalla jiragen ruwa biyu da ke wucewa mashigar Hormuz, lamarin da ya haddasa musayar wuta tsakanin Iran da Amurka, inda kowanne ɓangare ke zargin ɗaya da karya yarjejeniyar tsagaita wuta..

  2. Gwamnan Benue ya umarci a fara bincike kan kisan shugaban makiyaya

    Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya umarci hukumomin tsaro da su fara bincike nan take kan kisan shugaban ƙungiyar makiyaya ta MACBAN a jihar, Alhaji Ardo Risku, tare da abokinsa.

    Ya bayyana matuƙar kaɗuwarsa da alhini kan lamarin, yana mai cewa ya zo ne a wani lokaci da jihar ke fara samun zaman lafiya a yankuna daban-daban.

    Gwamnan ya ce wannan kisan ba wai kawai abin takaici ba ne, har ma wata ƙoƙari ce ta karya zaman lafiya da sulhun da gwamnatinsa ke ƙoƙarin tabbatarwa, musamman ganin cewa ya faru ne jim kaɗan bayan wani muhimmin taron tsaro.

    Saboda haka ya buƙaci a gudanar da bincike mai zurfi da gaskiya, tare da kamo waɗanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban shari’a

    Haka kuma ya yi kira ga al’umma su kwantar da hankalinsu, yana mai gargaɗin cewa bai kamata a bari masu anfani da rikici su tayar da tarzoma ba, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan.

  3. Adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasar Venezuela ya haura 1,400

    Adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasa mai ƙarfi guda biyu da suka afkawa ƙasar Venezuela ya haura 1,400, yayin da har yanzu ake ci gaba da ayyukan ceto.

    Kwana uku bayan afkuwar girgizar, ana neman mutane da dama da suka ɓace, yayin da jami’an agaji ke ci gaba da tono waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai.

    A lokaci guda, ƙorafe-ƙorafen jama’a na ƙaruwa kan yadda gwamnati ke tafiyar da lamarin.

    Wakilin BBC da ke garin La Guaira, wanda ya fi fuskantar iftila’in, ya ce halin da ake ciki na da matuƙar tsanani, inda har yanzu ba a san adadin mutanen da ke maƙale a ƙarƙashin gine-ginen da suka rufta ba.

    Ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa sun isa yankin, inda ƙungiyoyi daga ƙasashen Mexico, Brazil, da sauransu ke aiki ba dare ba rana wajen ceto da taimakawa waɗanda bala’in ya shafa.

  4. 'Wani jami'in Amurka ya tabbatar da harin Iran kan wuraren sojin ƙasar'

    Kamfanin dillancin labaran Reuters ya rawaito cewa wani jami’in Amurka ya tabbatar da cewa Iran ta harba makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuƙa zuwa wasu ƙasashe makwabta, ciki har da Bahrain da Kuwait.

    Tuni rundunar IRGC ta Iran ta sanar cewa ta kai hari kan wuraren sojojin Amurka, inda ta ce ta nufi sansanin Ali al-Salem da ke Kuwait, da kuma hedikwatar rundunar ruwa ta Amurka da ke Bahrain.

    Rundunar ta ce ta kai waɗannan hare-hare ne da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa.

  5. Ministan harkokin wajen Iran zai kai ziyara Iraq yau

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, zai kai ziyara ƙasar Iraq a yau Lahadi tare da wata tawaga ta diflomasiyya.

    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baghai, ya ce a yayin ziyarar, za a tattauna dangantakar ƙasashen biyu tare da nazarin halin da ake ciki a yankin da kuma duniya baki ɗaya, a tattaunawa da manyan jami’an gwamnatin Iraq.

    Ya ƙara da cewa ɓangarorin biyu za su yi musayar ra’ayi kan muhimman batutuwa da suka shafi siyasa da tsaro a yankin, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Iran da Iraq.

  6. Mun kai hari kan wuraren sojin Amurka guda 8 a Kuwait da Bahrain - Iran

    Rundunar juyin juya halin Iran IRGC ta Iran ta sanar cewa da safiyar Lahadi ta kai hari kan muhimman wuraren sojojin Amurka a ƙasashen Kuwait da Bahrain, ta da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙa.

    A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce ta kai harin ne a wurare takwas na sojojin Amurka, ciki har da sansanin jiragen sama na Ali al-Salem Air Base da ke Kuwait, da kuma hedikwatar rundunar ruwa ta Amurka ta Fifth Fleet da ke Bahrain.

    Rundunar ta IRGC ta ce wannan hari martani ne ga hare-haren da Amurka ta kai a baya.

    Sai dai har yanzu jami'an Amurka ba su yi tsokaci ba kan girman ɓarnar da aka yi ko yiwuwar asarar rayuka.

    Haka kuma IRGC ta zargi Amurka da kai hari kan sansanonin ruwan Iran guda biyar, tana mai cewa an yi hakan ne da sunan cewa rundunar ruwan IRGC ta tare wani jirgi.

    Sanarwar ta jaddada cewa bisa yarjejeniyar da aka cimma, Iran ce ke da alhakin kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, kuma daga yanzu rundunar IRGC za ta ɗauki matakai masu tsauri kan duk wani jirgin ruwa da ta ɗauka a matsayin “mai karya doka.”

  7. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu a shafinmu na BBC hausa kai tsaye barkanmu da safiyar yau Lahadi.

    Kamar dai yadda aka saba wannan shafi ne da zai kawo muku labarai na abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, da Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.