Sukuwar doki cikin tekun Atlantika

An wallafa

Ƙayatattun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata

.

Asalin hoton, anadolu

Bayanan hoto, Ɗan ƙabilar Masai yana busa ƙaho yayin bikin al`adun gargajiya a Kenya ranar Talata.
.

Asalin hoton, anadalo

Bayanan hoto, Wani ɗan Kabilar Maasai ya yi ado da kayan gargajiya
.

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, An harba abubuwa masu tartsatsin wuta a lokacin bikin Moussem na Moroko wanda ake gudanarwa kowacce shekara
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gudanar da sukuwar doki a tekun Atlantika, a ci-gaba da bukukuwan al`adun Moroko a ranar Talata.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙwararren ɗan wasan tseren kekuna Dillon Geary daga Afirka ta Kudu ya ɗauki alwashin yin nasara a gasar tseren kekuna ta duniya karo na 96 a Glasgow.
.

Asalin hoton, reuters

Bayanan hoto, Wasu mutane a kogi yayin tsananin zafi ranar Litinin a Masar.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Talata ƴar wasan Najeriya Destiny Nkemakonam Agbo na farin cikin nasarar da ta samu a wasannin matasa na Ƙasashe renon Ingila shekara ta 2023.
.

Asalin hoton, -

Bayanan hoto, Masu goyon bayan juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun yi dandazo a Niamey babban birnin kasar suna farin ciki.
.

Asalin hoton, Shutterstock

Bayanan hoto, Magoya bayan jam`iyyar Zanu-PF mai mulki a Zimbabuwe a lokacin gangamin jam`iyyar ranar Laraba a birnin Harare, za a gudanar da zabukan kasar ranar 23 ga watan Agusta.
.

Asalin hoton, anadolu

Bayanan hoto, Zaki yana hutawa a Maasai Mara na ƙasar Kenya, ranar Alhamis ce ranar Zakuna ta duniya.