Yadda mata a Kamaru ke rungumar tiyatar kwaskwarimar halitta

An wallafa

Tiyatar yi wa halittar jiki kwaskwarima, abin yayin zamani ne da ke ƙara ɗaukar hankulan mata a faɗin duniya, ciki har da ƙasar Kamaru.

'Yan mata ne dai aka fi tunanin a gaba-gaba wajen rungumar wannan baƙuwar ɗabi'a ta rige-rigen mallakar cikar surar 'ya mace daga dabaru da hikimomin likitoci.

Sai dai, mutuwar wata matashiya a baya-bayan nan cikin yankin Bafoussam, kwanaki ƙalilan da yi mata irin wannan tiyata, ta tayar da hankalin al'umma tare da sake haska girman illolin da tiyatar ke haddasawa a ƙasar.

Kafofin labaran Kamaru sun ce an yi wa matashiyar tiyata ne a farkon wannan wata na Agusta, tana muradin a daidaita mata surar damtse da diga-digai da kuma tumbinta.

Sai dai tiyatar, ta ya zo da akasi, inda matashiyar ta ce ga garinku nan a ranar Laraba, 16 ga watan Agusta.

Hukumomi dai sun fara gudanar da bincike, kan abin da ya yi sanadin mutuwar Prestige Victoire Kamdem Tiche, wadda aka gano an yi mata ɗinki a sassa da dama na jiki.

Rashin nasarar aikin tiyatar Prestige Victoire, ya zo ne kimanin wata bakwai da mutuwar wasu 'yan mata uku cikin watan Disamba a birnin Bafia na lardin tsakiya, su ma bayan an yi musu alluran ƙara cikar mace.

Mata masu yawa ne ke ƙulafucin samun shafaffen ciki da ƙirji hani'an da kuma kuturi fantsam mai sifar ɗaurin kalangu.

Suna koyi ne, akasari da fitattun taurarin fina-finai da mawaƙan zamani, ko da yake likitoci na gargaɗin cewa irin wannan kwaskwarimar halitta, tana da matuƙar hatsari.

Mata 'yan birni kan yi dashe ko gyara don ƙara ciko da nono, da zuƙe kitse ko reɗe tsoka daga tumbi ko wani sashen jiki da ba a buƙata, da ƙara girman ɗuwawu da cinyoyi kai har ma da sharaɓa.

Haka zalika, likitoci na iya tada komaɗar hanci ya koma ɗan firit, da canza fasalin leɓe ta yadda zai ƙara jan hankali, da raba fuska da kwarmi da taya-ni-munin da ba a buƙata.

A baya dai, masu sha'awar irin waɗannan ayyukan tiyata na tattaki zuwa ƙasashen waje, amma yanzu ana ƙara samun likitoci a cikin gida ko ƙasashe maƙwabta da ke tiyatar kwaskwarimar halitta kuma a cikin farashi mai rahusa.

A wasu lokutan da wuya a zargi matan da ke tiyatar kwaskwarima don canza fasalin halittar jikinsu.

Mata a ƙasashe da dama na fuskantar tsangwama, da gori har ma da kushen halitta daga ƙawaye ko samari da sauran abokan zama waɗanda ke tunanin cewa ba su "gama haɗuwa ba".

Wani masanin halayyar ɗan'adam a Kamaru, ya ce kafofin sadarwa irinsu talbijin da shafukan sada zumunta sun ba da gagarumar gudunmawa wajen sauya wa mata tunani game da yadda suke kallon jikinsu.

Dr. Didier Demassosso ya ce zamani ya nuna macen da ta fi ɗaukar hankali, ita ce wadda ƙirjinta yake cike, tana kuma da manyan mazaunai da katara mai cikar fasali. Fatar jikinta lamɓau ba tare da tamoji ko tattarewar shekaru ko cuta ba. Tana kuma da gashi har gadon baya, ga shafaffen ruwan ciki ba irin na wadda ta hayayyafa ba.

Da yake, su mata tun fil'azal, ma'abotan ado da kwalliya ne, a ko da yaushe suna duban abubuwan yayi.

A cewar, Dr. Didier Demassosso, da mata za su tsaya da iya kyawun da Allah ya yi musu kawai, su yi kwalliya da sanya sutura ta fita-kunya, hakan zai sanya a riƙa ganinsu a matsayin ababen sha'awa.

Ya kuma ce abu ne mai kyau mace ta san cewa idan ba ki da gashin wance, to ki haƙura da yin kitson wance. Sannan mace ta yarda haka, kuma ta yi alfahari da yadda Allah ya halicce ta.