'Na fi jin dadin haihuwar tiyata fiye da haihuwa da kaina'

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wani sabon bincike da aka wallafa a mujallar likitanci ta Plos Medicine na cewa yi wa mai nakuda tiyata a fitar da jariri na iya zama hanya mafi sauki idan an kwatanta da haihuwar mace da kanta, musamman ma matar da aka taba yi mata irin wannan tiyatar a baya.

Ana kallon kokarin mace na haihuwa da kanta zai iya haifar da matsala ga uwa da kuma jaririnta, idan an kwatanta da haihuwar tiyata.

Kwararru sun ce kamata ya yi a rika bai wa matan da za su haihu zabi kan hanyar da suka fi so su haihu idan da hali.

To, game da wannan al'amari, Tchima Illa Issoufou a Jamhuriyar ta yi kicibis da wata mai jego da ta taba haihuwar tiyata ko fashi, bayan haihuwa da kanta.