Gasar Kofin Duniya 2026: Me kuke son sani kan wasan Mexico da Afirka ta Kudu?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Mexico ɗaya daga kasashe ukun da za su gudanar da gasar Kofin Duniya a 2026, za ta yi bikin buɗe wasannin bana ranar Alhamis.

Za a fara da yin shagulgula da waƙe-waƙe dangane da babbar gasar tamaula ta duniya da kuma nuna al'adun Mexico.

Da zarar an kammala bikin, za a fara wasa tsakanin Mexico da kuma Afirka ta Kudu a katafaren filin wasan da ake kira Azteka a birni Mexico.

Wannan shi ne wasan farko a rukunin farko daga 104 da za a fafata tsakanin birane 16, inda Amurka take da 11 da Mexico mai uku da kuma Kanada mai biyu.

Wannan shi ne karon na biyu da tawagogin za su kece raini a tsakaninsu a gasar cin kofin duniya tun bayan 2010 da Afirka ta Kudu ta gudanar da wasannin.

Bafana-Bafana ta halarci gasar kofin duniya karo na huɗu, ta kuma kawo wannan matakin, bayan da ta ja ragamar rukuni na uku a shiyyar Afirka a wasannin neman gurbin shiga gasar - har da Super Eagles a cikin rukunin da ba ta kai bante ba.

Haɗuwa tsakanin Mexico da Afirka ta Kudu

Shekara 16 baya, Afirka ta Kudu da Mexico suka haɗu a wasan farko a gasar kofin duniya a 2010 da Afirka ta Kudu ta karɓi bakuncin wasannin, karon farko da nahiyar Afirka ta gudanar da wasannin babbar gasar tamaula ta duniya a tarihi

A karawar ce Siphiwe Tshabalala ya kafa tarihi, bayan wata ƙwallo mai kayatarwa da ya ci wa kasar, sai dai daga baya Mexico ta farke ta hannun Rafael Marquez aka tashi wasan 1-1.

Marquez yanzu yana mataimkain kocin tawagar Mexico, Javier Aguirre da za su fuskanci Afirka ta Kudu.

Shi kuwa kociyan Afirka ta Kudu, Hugo Broos ya buga wa Belgium gasar kofin duniya a 1986, inda suka kece raini da Mexico a wasannin cikin rukuni, daga baya suka yi na huɗu a gasar.

Mai masukin baƙi Mexico na fatan doke Afirka ta Kudu ya zamana ta ci wasan farko a gasar kofin duniya daga karawa bakwai baya da ta buga.

To sai dai sun haɗu tun kafin nan:

Concacaf Gold Cup

South Africa 2 - 1 Mexico ranar 8 ga watan Yulin 2005

Wasan sada zumunta

Mexico 4 - 2 South Africa ranar 6 ga watan Yunin 2000

Wasan farko a rukunin farko

Wannan shi ne karo na uku da Mexico ke karɓar bakuncin gasar kofin duniya,

Kuma koci, Javieh Aguirre zai dogara da matasan ƴan ƙwallo da kuma masu ƙwarewa da ya haɗa da mai taka leda a Fulham, Raul Jimenez da kuma gogaggen mai tsaron raga, Guillermo Ochoa, wanda zai buga gasar kofin duniya karo na shida.

Daga cikin ƴan wasan har da matashi mai shekara 17, Gilberto Mora, wanda shi ne mafi kuruciya a gabaki ɗayan ƴan ƙwallon da za su buga wasannin bana.

Ita dai Mexico na fatan wuce gurbin kwata fainal, wanda shi ne ƙwazon da take alhari da shi da taɓa takawa a tarihin babbar gasar tamaula ta duniya.

A gasar bana, golan Mexxico Ochoa da ƙyaftin din Argentina, Lionel Messi da kuma na Portugal, Cristiano Ronaldo za su buga gasar kofin duniya karo na shida, inda ake sa ran kowanne zai yi ban kwana da zarar an kammala wasannin bana.

Afirka ta Kudu kuwa, wadda dk da ɗebe mata maki ukun da aka yi, saboda an same ta da yin amfani da ɗan ƙwallon da bai cika ka'ida ba, ta samu gurbin shiga gasar kofin duniya a karon farko tun bayan 2010, bayan da ta ci Rwanda 3-0 a wasan karshe a cikin rukuni shiyyar Afirka a cikin Oktoban 2025.

Wannan shi ne karo na huɗu da Bafana-Bafana, wadda akae kira "The Boys" a harshen Zulu za ta halarci gasar kofin duniya, wadda har yanzu ba ta taɓa haura wasannin cikin rukuni ba

Ɗaya daga ɗan wasan da ake sa ran zai haska a tawagar ta Afirka ta Kudu ya haɗa da mai taka leda a Orlando Pirates, Relebohile Mofokeng.

Me kociyoyin suka ce tun kafin su fuskanci juna?

"Ban taɓa jin wani babbar farin ciki a cikin shekara 50 da na shafe ina buga ƙwallon ƙafa kamar yadda na ji da jan jagoranci kasata a gasar cin kofin duniya da za muyi a gida ba. Na yi abubwa da yawa a fannin rayuwata, amma wannan abin ba zan manta da shi ba. Wannan shi ne abin da na gaya wa ƴan wasan, kuma ina ganin na sun gamsu da kalamai na. Suna jin daɗi sun kuma samu natsuwa da kwanciyar hankali; wannan abu ne mai matuƙar mahimmanci, kuma ƴan wasan sun daɗe suna wakiltar kasar, sun zama tamkar iyalai. Na kuma fahimci hakan, domin na gani karara." in ji kociyan Mexico, Javier Aguirre.

''Mexico ce babbar barazana a rukunin mu, saboda haka wasan zai yi zafi a wajenmu. Ina son na tabbatar muku da cewa tawaga ta a shirye take, za kuma mu saka ƙwazo tun daga lokacin da aka take leda har zuwa a tashi daga karawar. Daga nan sai mu san abin yi. In ji Mai horar da tawagar Afirka ta Kudu, Hugo Broos.

Ƴanwasan da ake sa ran za su fara buga fafatawar

Ƴan Mexico 11 da ake sa ran fara wasan da su:

Rangel; Gallardo, Vasquez, Montes, Reyes; Gutierrez, Lira, Fidalgo; Quinones, Alvarado, Jimenez

Ƴan Afirka ta Kudu 11 da ake sa ran fara wasan da su:

Williams; Mudau, Okon, Mbokazi, Modiba; Mokoena, Sithole, Mbatha; Moremi, Foster, Appollis