Harris da Walz sun ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, da abokin takararta, wanda zai zamo mata mataimaki, Tim Walz sun bayyana a karon farko domin fara yaƙin neman zaɓe a Philadelphia.

Kamala Haris ta shaidawa taron magoya bayan jam’iyyar Democrat cewa gwaman abokin takarar nata, kuma Minnesota yana da ƙwarewar da ake buƙata domin taimaka mata wajen aiwatar da manufofin gwamnatinta.

Kafin bai wa Mr Walz damar yin jawabi ga magoya bayan su, Ms Harris ta ɗauki lokaci tana zayyana irin nagartar abokin takarar nata, da irin ayyukan da ya yi a rayuwarsa, a matsayin tsohon malamin makaranta, tsohon soja, kuma tsohon kocin ƙwallo, wanda kuma ta ce yanzu haka ke jan zaren sa a matsayin gwamnan Minnesota.

Wannan ne zangon farko, a jerin tarukan gangamin yaƙin neman zaɓe da ƴan takarar jam’iyyar Democrat suka tsara yi cikin kwana huɗu, a jihohin da ake sa ran kai ruwa-rana tsakanin dukkan jam’iiyun.

A tare Kamala Harris da Tim Walz suka bayyana a gaban magoya bayan su, kuma kai tsaye ƴar takarar shugaban ƙasar ta gabatar da wanda take fatan ya zama mataimakin ta.

"Tun daga ranar da na sanar da aniyata ta tsayawa takara, na fara faɗi-tashin zaƙulo wanda za mu yi aiki tare domin cimma nasarar aiwatar da manufofin ci gaban Amurka. Na zaɓo jagora wanda zai taimaka wajen haɗa kan ƙasar mu da ciyar da ita gaba, kuma ɗan kishin ƙasa, kamar dai yadda na yi wa Amurkawa alƙawari. A tare za mu cika alƙawarin samar da ƴanci da adalci ga kowa.’’

Ana dai ganin Mr Walz a matsayin ɗan siyasa da zai iya janyowa takarar jam’iyyar Democrat dimbin masu kaɗa ƙuri’a a tsakanin ma’aikatan Amurka.

A nasa jawabin, Mr Walz ya jinjinawa Ms Haris a kan dagewar ta wajen zaɓen wanda zai yi aiki tare da ita a shugabancin Amurka.

"Ta yi amanna da baiwa kowa ƴancin bunƙasa domin zama wani abu a cikin al’umma. Ta yarda da aiki tare wajen ciyar da Amurka gaba. Abin da ya rage kawai shi ne mu yi yaƙi tare, domin kuwa idan muka yi wannan yaƙi tare to za mu yi nasara.’’

Ms Harris da Mr Walz za su yi jawabi a babban taron jam’iyyar Democrat na ƙasa, wanda zai gudana daga ranar 19 zuwa 22 ga watan Ogustan bana, a Chikago.

Ƙuri’ar jin ra’ayi na nuna cewa Kamala Haris na ƙara karɓuwa a tsakanin Amurkawa, tun bayan da shugaban Biden ya sanar da janyewarsa daga takarar a watan da ya gabata.