Potter ya fara jan ragamar Chelsea a Premier da kafar dama

Chelsea vs Palace

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Sabon kocin Chelsea, Graham Potter ya fara da cin wasan Premier a karon farko da ya ja ragamar kungiyar Stamford Bridge a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Ranar Asabar Chelsea ta yi nasara a kan Crystal Palace da ci 2-1 a Selhurst Park karawar mako na takwas a Premier League.

Minti bakwai da fara wasa Palace ta ci kwallo ta hannun Odsonne Edouard, daga baya Pierre-Emerick Aubameyang ya farke tun kan su je hutun rabin lokaci.

Dan wasan tawagar Gabon ya kafa tarihin cin kwallo a wasansa na farko a Arsenal, yanzu kuma a Chelsea.

Kungiyar Stamford Bridge ta sayo tsohon dan kwallon Arsenal a bana daga Barcelona karkashin Thomas Tuchel.

Potter ya maye gurbin Tuchel, bayan kasa taka raar gani a kakar bana duk da makudan kudin da kungiyar ta kashe wajen sayo sabbin 'yan wasa a bana.

Daf da za a tashi daga wasan ne Conor Gallagher ya ci wa Chelsea na biyu da ta hada maki ukun da take bukata.

Wannan shi ne wasa na biyu da Potter ya ja ragamar Chelsea, bayan tashi 1-1 da RB Salzburg a Champions League.

Da wannan sakamkon Chelsea ta hada maki 13, bayan cin wasa hudu da canjaras daya da shan kashi a biyu.

Kungiyar Stamford Bridge za ta buga wasa na gaba da AC Milan a Champions League.

Palace wadda karawa daya ta ci a bana da canjaras uku, ta yi rashin nasara wasa uku da makinta shida kenan.

Za kuma ta kece raini da Leeds United a wasanta na gaba a Premier League.