United za ta yi wasa a Malaysia da Hong Kong idan an kare kakar bana

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta buga wasanni a Malaysia da Hong Kong da zarar an kammala gasar Premier League a watan Mayu.
United za ta kara da fitattun ƴan wasan Asia a Kuala Lumpur ranar 28 ga watan Mayu daga nan ta ziyarci birnin Hong Kong kwana biyu tsakani.
United za ta ziyarci nahiyar Asia da zarar ta buga wasan karshe a gida da Aston Villa a Premier League ranar 25 ga watan Mayu.
Ana sa ran United za ta samu kuɗi da zai kai £7.8m a ziyar da za ta kai da wasannin da za ta buga a Asia.
Daga nan kuma ƙungiyar da Ruben Amorim ke jan ragama, za ta je Amurka daga ranar 26 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Agusta, domin buga wasannin tunkakar kakar baɗi.
United tana da magoya baya da yawa a Malaysia, kuma tana da hulɗar zirga-zirga da kamfanin jirgin sama na Malaysia.
Rabon da United ta ziyarci Malaysia tun 2009, wadda ta buga wasanni a Hong Kong a 2013.
A bara kan fara kakar bana, Tottenham da Newcastle United, sun yi wasanni a Austalia.
Har yanzu ana ta kukan cewar wasa yana yi wa ƴan ƙwallo yawa, bayan da aka kara yawan ƙungiyoyi a Fifa Club World Cup, an kara wasanni a Champions League da sauran gasar Turai.
Hakan ne ya sa Ingila ke buga wasa zangon farko a FA Cup, maimakon gida da waje da ake yi a baya, domin a rage yawan wasannin da ƴan ƙwallo ke buga wa.












