Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za mu sa Liverpool ta yi ta jira kafin lashe Premier - Arteta
Mikel Arteta ya ce Arsenal za ta sa Liverpool ta yi ta jiran ranar da za ta lashe Premier League na bana, ba dai a wannan ranar Lahadin ba.
Za a bai wa Liverpool kofin Premier a lokacin da zai rage saura wasa biyar-biyar a kare kakar nan da zarar Arsenal ta yi rashin nasara a hannun Ipswich, ita kuwa Liverpool ta doke Leicester City a King Power.
Sai dai Arteta, wanda ya fitar da Real Madrid a Champion League ya ce zai yi nasara a kan Ipswich, hakan zai sa Liverpool ta ci gaba da jiran ranar da za ta lashe kofin bana.
A kakar bara haka Arsenal ta yi ta jan kafar Manchester City har sai a ranar karshe da aka tabbatarwa da City kofin Premier League.
Sai dai a kakar nan Arsenal ta kasa sa ƙwazo kamar yadda ta yi a bara, duk da tana mataki na biyu a teburi, Liverpool ta ba ta tazarar maki 13 tsakani.
Gunners za ta je Portman Rood da tazarar maki 13 tsakaninta da Liverpool, bayan da Arsenal ta yi canjaras biyu a jere da Everton da kuma Brentford.
Wadda take ta ukun teburi, Newcastle United, za ta fuskanci Arsenal a ranar karshe a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Newcastle ta ci wasa biyar a jere, kuma zai rage tazarar maki daya tsakani da Arsenal, idan ta yi nasara a hannun Aston Villa ranar Asabar.
Ipswich za ta yi ban kwana da Premier League zuwa Championship a baɗi da zarar ta kasa samun maki a kan Arsenal.
Arsenal za ta buga daf da karshe a Champions League da Paris St Germain a Emirates ranar 29 ga watan Afirilu, sannan mako ɗaya tsakani a buga karawa ta biyu a Farana.
Arsenal da Paris St German ba wadda ta lashe Champions League a tarihi.