Shagunan kasuwancin da ba sa bari mutane su manta da ƙasashensu na asali

Vijaya Popat (a tsakiya) ta buɗe shagonta a 2011

Asalin hoton, Popat Mithai & Farsan

Bayanan hoto, Vijaya Popat (a tsakiya) ta buɗe shagonta a 2011
    • Marubuci, Daga Dhruti Shah
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC kan Kasuwanci
  • An wallafa

A shagon da danginta ke lura da shi mai suna Popat Mithai & Farsan, Popat da 'yan uwanta kan shafe lokaci suna hulɗa da kwastomomi a harsuna daban-daban har ma ba sa samun lokacin da za su zauna su huta, balle ma hira da 'yan jarida. 

Mrs Popat ta kafa kasuwancin ne a Leicester, Birtaniya a 2011 don sayar da alawowi da kayan maƙulashe na Indiyawa kuma ya haɓaka daga ma'aikata biyu zuwa 15.  Sun ƙaddamar da shafin sayayya ta intanet a 2018.

Hadahada ta hauhawa a lokacin annobar korona daidai lokacin da kwastomomi ke neman abinci mai sauƙi - nau'in wanda suke kawowa daga ƙasashen Indiya da Pakistan da Bangladesh da Sri Lanka.

Ɗan Popat mai suna Shyam ne ya yi magana da BBC a madadin tawagar. "Mahaifiyata ta shahara a wannan unguwar a matsayin 'yar kasuwa," in ji shi.

"Kuma kowa na son ya yi magana da ita saboda ta samo masa wani nau'i na kaya." 

Kasuwancin Popat Mithai & Farsan da ake yi ta intanet na bai wa shagon damar biyan buƙatar mazauna Birtaniya baki ɗaya

Asalin hoton, Popat Mithai & Farsan

Bayanan hoto, Kasuwancin Popat Mithai & Farsan da ake yi ta intanet na bai wa shagon damar biyan buƙatar mazauna Birtaniya baki ɗaya

Ya ƙara da cewa ba iya waɗanda suka je Birtaniya tsawon lokaci ba ne ko kuma waɗanda ba su daɗe da zuwa ba kwastomomin nasu.

"A lokacin dokar kulle, shafinmu na intanet ya ceci rayuwar mutane da dama, yanzu kuma da muka fita daga dokar ya zama babban kasuwanci a kan kansa," in ji Shyam Popat. "Yanzu cinikin da ake yi ta intanet ya kai kusan kashi 1 ko 2 cikin huɗu na ribar da ake samu."

Baya ga kayayyakin da suke kaiwa daga Kudancin Asiya, suna sayo kaya daga Kenya.

A baya-bayan nan, gwamnatoci na sane da cewa gudunmawar da mazauna ƙasashen ƙetare ke bai wa tattalin arzikin ƙasashensu na asali, wanda da wuya a iya kwatanta shi.

Abincin Pizza ya shahara a duniya sakamakon ciranin da 'yan Italiya suka yi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Abincin Pizza ya shahara a duniya sakamakon ciranin da 'yan Italiya suka yi
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yanzu haka akwai mutum aƙalla miliyan 281 da ke cirani a ƙasashen da ba nasu na asali ba, a cewar rahoton Cirani na Duniya na 2022 da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar ta hannun sashen International Organization for Migration (IOM).

Wannan adadi ya kai kashi 3.6 cikin 100 na yawan al'ummar duniya, ko kuma 1 cikin duk mutum 30. Babu 'ya'yan waɗannan mutane a cikin lissafin ko kuma 'yan uwan 'yan ciranin.

Wani abu da ya tabbata shi ne cewa ƙarfin niyyar 'yan cirani wajen yin kasuwanci a fili yake. Wani rahoto da cibiyar Organisation for Economic Co-operation and Development ta fitar a 2010 ya ce 'yan kasuwa 'yan cirani sun fi ilimi sama da tsaransu 'yan ƙasa, kuma sun fi samun yiwuwar kafa sabon kasuwanci. Shagon Vijaya Popat da ire-irensa na taka rawa wajen haɓaka darajar kayan da Indiyawa ke shigarwa Birtaniya zuwa dala biliyan 10.4 a shekarar da ta gabata.

Shi ma Olivier Habiyambere da ke zaune abirnin Paris na taimakawa wajen fitar da kayayyakin Kenya zuwa Turai.

Shi ne ya kafa dandalin Kenyan Diaspora Market da ke safarar abinci da tufafi daga ƙasar sannan kuma ya sayar wa kwastoma a Turai.

Olivier Habiyambere ya ce ciniki a Kenyan Diaspora Market na haɓaka ne saboda yadda mutane ke bai wa abokansu labari

Asalin hoton, Olivier Habiyambere

Bayanan hoto, Olivier Habiyambere ya ce ciniki a Kenyan Diaspora Market na haɓaka ne saboda yadda mutane ke bai wa abokansu labari

Mr Habiyambere da ya tashi a Kenya, ya yi tunanin kafa kasuwancin ne lokacin da ya koma birnin Paris don ya yi karatu inda kuma ya haɗu sauran 'yan Kenya.

"Kowa na rububin kayan Kenya, amma matsalar ita ce yadda za a kai kayan zuwa nan daga Kenya," a cewarsa. "Mutane za su iya samun kayan idan suka je Kenya amma matsalar ba duk shekara suke zuwa ba."

Saboda haka ne ya kafa kasuwancin a watan Afrilun 2022 don samar wa Kenya mazauna Turai hanya mai sauƙi wajen sayen kayayyaki daga gida.

Mista Habiyambere ya ce kasuwancin nasa ya girma saboda taimakon da yake samu daga 'yan Kenya bayan an ba su labari a zaurukan dandalin zumunta na WhatsApp.

'Yan Kenya kan sayar da kayayaki irin waɗannan a ƙasashen da suke zaune

Asalin hoton, Kenyan Diaspora Market

Bayanan hoto, 'Yan Kenya kan sayar da kayayaki irin waɗannan a ƙasashen da suke zaune

Duk da cewa 'yan Kenya na mayar da hankali kan kayan ƙasarsu, shagon Agora Greek Delicacies da ake birnin Glasgow na da kwastomomi daga wasu sauran sassa fiye da 'yan ƙasar Girka.

Wasu ma'aurata ne suka kafa shi kusan shekara 10 da suka wuce. Christina Lyropoulou da mijinta Michael Sofianos sun je karatun jami'a ne a Birtaniya. Yanzu suna da ma'aikata 14 kuma suna shigar da abincin Girka a wuraren cin abinci.

"Mun fara faɗaɗa harkar a Birtaniya da kuma matafiya zuwa Girka ko masu abokai a Girka," in ji Ms Lyropoulou.

"Cinikin da shagonmu ya samu ya ninka a watan farko da aka saka dokar kulle."

Christina Lyropoulou ta samu ciniki sosai a lokacin annobar korona

Asalin hoton, Christina Lyropoulou

Bayanan hoto, Christina Lyropoulou ta samu ciniki sosai a lokacin annobar korona