Southampton ta amince da ɗaukar Ramsdale daga Arsenal

Goalkeeper Aaron Ramsdale reacts after making a save for Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Aaron Ramsdale na cikin tawagar Ingila a gasar Euro 2024 da aka kammala a Jamus
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Southampton ta amince da ɗaukar mai tsaron ragar Arsenal, Aaron Ramsdale, kan fan miliyan 25.

Ana sa ran Ramsdale mai shekara 26 zai kammala komawa can kafin ranar Juma'a, wadda ita ce rana ta ƙarshe da za a rufe kasuwar cinikayya da musayar 'yan wasa ta farkon kaka.

Kociyan ƙungiyar da ake yi wa laƙabi da Saints, Russell Martin, ya faɗa wa BBC cewa: "Idan cinikin ya faɗa abu ne na murna sosai.

"Amma dai dole mu jira mu gani. Ina tabbacin za mu yi magana a kan hakan da zarar an kammala."

Kafin yanzu Wolverhampton Wanderers ce kan gaba wajen ɗaukar golan na Ingila, wanda David Raya ya ƙwace masa hannu a Arsenal ɗin.

Sai dai Wolves ta janye ne saboda ɗan wasan ya yi mata tsada.

Ramsdale ya buga dukkan wasannin kakar 2022-23 yayin da Arsenal ta ƙare a mataki na biyu, amma kuma ya rasa damarsa bayan Raya ya koma Emirates daga Brentford a kakar wasan da ta gabata.