Maganar komawar Haaland Real Madrid “ba gaskiya ba ne”

Haaland na da kwallo 14 a gasar Premier ya zuwa yanzu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Haaland na da kwallo 14 a gasar Premier ya zuwa yanzu
An wallafa

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce rahotanni da ke fitowa daga Sifaniya kan cewa Erling Haaland zai koma Real Madrid ba gaskiya ba ne.

Kocin ya musanta cewa cikin cinikin dan wasan babu kudin da za a biya idan zai koma Madrid a 2024.

Da yake magana bayan da dan wasan ke ci gaba da zuba kwallaye a raga, inda ya ci Copenhagen kwallo biyu a Champions, kocin ya musanta rade-radin cewa Real Madrid da Haaland sun cimma yarjejeniya a matakin shi da su.

Maganar komawar Haaland Real Madrid “ba gaskiya ba ne”

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Maganar komawar Haaland Real Madrid “ba gaskiya ba ne”

“Ba gaskiya bane” in ji Guardiola “babu wasu kudi da za a biya in zai koma Madrid ki wata kungiya ta daban. “Jita-jitar ta batan rai ne ? Aa ki kadan, mutane na ta cewa ba zan iya shawo kan wannan magana ba, to dole mu zama masu mayar da hanakali kan abin da muke da iko da shi.

“Abu Mafi mahimmanci shi ne ya saje da salon kungiyar tun bayan zuwansa, kuma ina jin cewa yana cike da farin ciki zamansa a nan, wannan ne ya fi komai mahimmanci.”

Ya zuwa yanzu dan wasan ya ci kwallo 19 a wasa 12 da ya buga tun bayan komawarsa Manchester City daga Borussia Dortmund.