An haɗa Real Madrid da Leganes a Copa del Rey a kwata fainal

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta fafata da Leganes, yayin da Barcelona za ta je Valencia a zagayen kwata fainal a Copa del Rey, bayan da aka raba jadawali ranar Litinin.
Wani wasan da zai yi zafi shi ne tsakanin Atletico Madrid da Getafe, yayin da za a yi tata burza tsakanin Real Sociedad da Osasuna.
Ana sa ran buga wasannin da za a gudanar ranar 5 ga watan Fabrairu.
A jadawalin ya bayar da damar sake buga El Clasico wato karawar hamayya tsakanin Real da Barcelona a wasan karshe da suka daɗe ba su haɗu a gasar tsawon shekaru.
An haɗu a wasan karshe a Copa del Rey karawar El Clasico sau 18, Real ce ta yi nasara 11 daga ciki, wasan baya bayan nan da suka kara shi ne a 2014.
Kuma Real Madrid ce ta lashe kofin da cin 2-1 a wasan da aka yi a Valencia.
Sai dai a kakar bana, Barcelona ta caskara Real Madrid karo biyu a baya, wadda ta fara cin 4-0 a Santiago Bernabeu cikin watan Oktoban 2024.
Sai kuma Barcelona ta lashe Spanish Super Cup na bana a kan Real Madrid da cin 5-2 a Saudi Arabia a makon jiya.
Real Madrid ce kan gaba a teburin La Liga da maki 46, sai Atletico Madrid ta biyu da kuma Barcelona ta uku da tazarar maki makwai tsakani da Real.











