Copa del Reay: Real Madrid da Deportiva Minera ranar Litinin

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid tana shirin buga Copa del Rey da Deportiva Minera ranar Litin zagayen ƴan ƙungiyoyi 32 a filin Cartagonova.

Ranar Juma'a Real Madrid ta doke Valencia a ƙwantan wasan La Liga, hakan ya sa ta ɗare kan teburin gasar.

Tun da sanyi safiya, Real Madrid ta fara yin atisaye a shirin da take na yin abin kirki a Copa del Rey na bana.

Dukkan ƴan wasan da suka fuskanci Valencia sun motsa jiki, sauran suka yi na su karkashin Antonio Pintus.

Daga baya aka raba filin biyu aka ci gaba da murza leda tsakanin ƴan wasa, sannan aka karkare da bugun tazara da lailaya ƙwallo.

Arda Gula ya mota jiki shi kaɗai a kokarin da yake na komawa kan ganiya, bayan rashin lafiya.

Shi kuwa Alaba ya motsa jiki tare da sauran ƴan wasa, yayin da Carvajal da Militao suka yi na su atisayen da ban.

Wasannin da za a buga a Copa del Rey ranar Lahadi:

  • Elche da Las Palmas
  • Ourense da Valladolid
  • Cartagena SAD da Leganes
  • Ponferradina da Real Sociedad
  • Racing Santander da Celta Vigo

Ranar Litinin 6 ga watan Janairu

  • Deportiva Minera da Real Madrid