Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rodri ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2024
Ɗan wasan tsakiya na Manchester City da Sifaniya Rodri ya lashe kyautar Ballon d'Or ta maza - wanda aka baiwa gwarzon dan ƙwallon ƙafa na bana.
Ɗan wasan mai shekaru 28, wanda ya yi rashin nasara a wasa daya kacal a kakar wasan da ta gabata a kulob ɗin da kuma ƙasarsa, an ba shi kyautar ne a birnin Paris bayan ya taimakawa Spain ta lashe gasar Euro 2024 a watan Yuli.
Ya kuma lashe gasar Premier da Uefa Super Cup da kuma gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyi tare da City.
Rodri shi ne ɗan wasa na farko a tarihin ƙungiyar da ya lashe kyautar Ballon d’Or.
Aitana Bonmati ta ƙasar Sifaniya ce ta lashe kyautar a bangaren mata, karo na biyu a jere, sai kuma Real Madrid ta lashe kyautar kulob na bana kuma kocinta Carlo Ancelotti shi ne ya lashe kyautar gwarzon kocin na bana, amma babu wani daga ƙungiyar da ya samu hartar bikin.
Kafin fara bikin an ruwaito cewa Real Madrid ta yi wa bikin tawaye bayan da aka ruwaito cewa ɗan wasanta Vinicius Jr ba zai lashe kyautar ba.
Wannan dai shi ne karon farko tun shekara ta 2003 da babu wanda ya lashe kyautar sau takwas Lionel Messi, mai shekaru 37, ko kuma wanda ya lashe sau biyar Cristiano Ronaldo, mai shekaru 39, a cikin jerin sunayen waɗanda ka iya lashe kyautar ba.
Rodri ya fice ne a lokacin hutun rabin lokaci a wasan ƙarshe na gasar Euro da Ingila, amma ya riga ya yi abin da ya dace don a lashe kyautar ta bana.
Sai dai kuma ba a tunanin zai buga sauran wasannin kakar 2024-25 bayan raunin da ya ji a wasan da suka tashi 2-2 da Arsenal a farkon kakar wasa ta bana.