Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwamnan Delta Oborevwori ya koma APC
Gwamnan jihar Delta da ke yankin Neja Delta a kudancin Najeriya, Sheriff Oborevwori ya fice daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa jami'yyar APC mai mulki a ƙasar.
Wani hadimin gwamnan ne ya tabbatarwa da BBC hakan a wata da tattaunawa da wayar tarho.
Oborevwori ya fice ne bayan wata tattaunawa da masu ruwa da tsaki da ya gudana a fadar gwamnatin jihar da ke Asaba.
Gwamnan wanda ya lashe zaɓe a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP ya samu tarba daga wajen manyan ƴan siyasa na jam'iyyar APC a wani mataki da ake kallo na da nasaba da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da ke tafe.
Bayanai sun ce gwamnan ya koma ne tare waɗansu manyan 'yan siyasa a jihar, ciki har da tsohon gwamnan jihar wanda ya yi wa PDP takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Ifeanyi Okowa.
Wani jigo a siyasar jihar ta Delta kuma dan majalisar dattawa, Sanata James Manager wanda ya karanta sanarwar bayan taro ya ce "Duka mambobin PDP a jiha da suka haɗa da gwamna da tsohon gwamna Okowa da shugaban majalisa da shugaban jam'iyya da shugabannin ƙananan hukumomi duk sun amince su koma APC".
Ko PDP za ta kai labari a zaɓen Najeriya na 2027?
Ficewar gwamnan Delta da kuma waɗansu da ke tafe ya sa wasu ƴan Najeriya sun fara ɗiga ayar tambaya kan makomar jam'iyyar a zaɓen 2027.
Hakan ya ƙara fito da irin ɓarakar da ke tattare da jam'iyyar PDP.
A kwanakin da suka wuce ne gwamnonin PDP suka yi watsi da yunƙurin haɗaka da sauran jam'iyyun hamayya ba da nufin tunkarar zaɓen 2027.
Matsayar gwamnonin ta ci karo da iƙirarin tsohon ɗantakarar jam'iyyar kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar inda a kwanakin baya ya ce yana yunƙurin ƙulla haɗaka da wasu jam'iyyu.
Masana siyasa a Najeriya na ganin matsayar gwamnonin jam'iyyar PDP tana da ɗaure kai musamman yadda wasu ke ganin ba za ta iya kai labari ba idan ba ta haɗa kai da sauran jam'iyyun hamayya ba saboda rikicin cikin gida da ya dabaibaye ta.
Farfesa Abubakar Kari na Jami'ar Abuja ya ce "Jam'iyyar na cike da rikici kuma a yanzu ƙarfinta ya ragu, yana da wahala ta iya cin zaɓe."
Masanin ya ce irin wannan saɓani na zaman ƴanmarina a PDP da sauran jam'iyyun hamayya, na nuna jam'iyya mai mulki ce za ta fi cin gajiyarsa musamman na ganin jam'iyyun hamayya ba su haɗe ba.