Abin da ƴan Najeriya ke cewa kan ƙarin albashin ƴan siyasa

An wallafa

Hukumar tarawa da rarraba kudin haraji ta kasa ta ce ta kammala shiri domin sake duba albashin masu rike da mukaman siyasa, da ma'aikatan shari'a, domin dacewa da halin da kasar ke ciki.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce a yanzu ana aiki ne da dokar da aka tsara tun shekarar 2008, wadda ta yi la'akari da yanayin da ake ciki lokacin da aka tsara dokar.

Sanarwar ta ambato shugaban hukumar Engr. Elias Mbam na cewa za su sake duba albashin zababbun shugabanni da masu rike da mukaman siyasa, kama daga shugabannin kananan hukumomi da kansiloli, da gwamnoni da kwamishinoni, da kuma albashin shugaban kasa da mataimakinsa da kuma 'yan majalisun jiha da na tarayya.

Mista Mbam ya ce hakkin hukumar ne ta tsara albashin zababbun shugabanni da masu rike da mukaman siyasa, tun daga matakin kananan hukumomi da zuwa matakin tarayya.

Haka kuma sanarwa ta ce aikin hukumar ya shafi zababbu da masu masu rike da mukaman siyasa, ban da albashin sauran ma'aikatan gwamnati, wanda hukumar ta ce ke hannan ma'aikatar tsara albashi ta kasa

Ƙungiyar ƙwadago ta yi Allah-wadai da matakin

To sai dai kungiyar kwadago ta kasar ta nuna rashin jin dadinta game da matakin, tana mai cewa babu wadanda suka fi cancantar karin albashi a kasar kamar ma'aikatan gwamnati.

Tana mai cewa a halin yanzu masu rike da mukaman siyasa sun fi kowa samun albashi mai gwabi a kasar.

Me sauran al'umma ke cewa?

Da alama labarin ƙarin albashin ga ƴan siyasa bai yi wa wasu masu amfani da shafukan sada zumunta daɗi ba.

Wani mai amfani da shafin tuwita @Pshuah ya ce "masu kuɗi suna ƙara azurta kansu, yayin da sauran ma’aikata da al’ummar Najeriya ke cikin wahala."

Wani mai suna “josephIfenyiC7 kuwa cewa ya yi "kalli yadda mutane ke shan wahala, amma su kuma suna batun ƙara wa kansu albashi.”

Albashin ma’aikata na daga cikin abubuwan da suke haifar da cece-ku-ce a Najeriya.

Bayanai na cewa yanzu haka akwai jihohi da dama na ƙasar waɗanda ba su fara aiwatar da ƙarancin albashi na naira dubu 30 ba ga ma’aikatansu.

Ko a kwakanin baya sai da ƙungiyar ƙwadago reshen jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin aiwatar da tsarin ƙarancin albashin na naira dubu 30, inda daga baya gwamnatin jihar ta yi alƙawarin aiwatarwa.