Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mazauna Uttarakhand a Indiya na cikin fargaba kan tsagewar bangon gidajensu
Mazauna garin Joshimath na neman gwamnati da ta sauya musu matsuguni da kuma gyara gidajensu bayan da yawancin gidajen ke tsassagewa.
A ranar Alhamis ne jami’ai suka dakatar da ayyukan da ake yi a garin bayan da dubban masu zanga-zanga suka toshe wata babbar hanya a jihar Himalaya.
Karamin ministan cikin gida a jihar na jagorantar wani gagarumar zama a ranar Juma’a don tattauna batun.
A makon nan ne aka kwashe gomman mutane zuwa wurare na wucin gadi.
Shugabannin al’umma a garin sun ce sama da gidaje 500 ne suka tsage a yankin sakamakon nutsewa da suke yi.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba – inda ko da a shekara ta 1976, wani kwamiti da gwamnati ta kafa ya ce garin Joshimath na cikin barazanar nutsewa bayan mazauna garin sun yi korafin cewa gidajensu na tsagewa.
Rahoton da kwamitin ya fitar, ya kuma yi gargadi kan barin ana gudanar da manyan ayyuka a yankin.
Amma shekaru goma bayan nan, ana samun ƙaruwar gine-gine a jihar Uttarakhand da ke makwabtaka da yankin Himalaya.
Jihar dai tana dauke da manyan wuraren bauta na ‘yan addinin Hindu, wuri kuma da miliyoyin mutane ke zuwa a kowace shekara don yin ibada.
Masana harkar gine-gine sun ce yawaitar ayyukan gini da ake yi na shafar yanayin muhalli na yankin, wanda kuma zai iya janyo girgiza ko kuma zaizayar kasa.
A ranar Alhamis ne jami’an gudanar da ayyuka a yankin suka dakatar da yin aiki, ciki har da aikin gyara babbar hanyar nan da za ta kai ga wurin bauta ta ‘yan addinin Hindu na Char Dham, har sai zuwa nan gaba.
A watan Oktoba ne wakilin BBC Vineet Khare ya kai ziyara garin na Joshimath inda ya tattauna da mazauna garin da ke zama cikin fargaba.
"Da zarar an fara ruwan sama, muna fita daga cikin gidajenmu saboda tsoro,’’ a cewar Sumedha Bhatt, wata da ke zama a ƙauyen Ravigram.
A waccan ziyara da BBCn ta kai, ta gano cewa yawancin mutane sun fara barin gidajensu saboda tsagewar da gidajensu ke yi na ƙaruwa sakamakon mamakon ruwan sama.
Wasu iyalai kuma sun koma yin wasu dabaru kamar amfani da ledoji da itatuwa domin tare ruwa da kuma kare gidajensu.
Masanin ma’adinai da ke cikin kasa, Swapnamita Vaideswaran, da ke amfani da na’urar tauraron dan adam don duba irin tsagewar da gidajen ke yi, ta ce aikin da ta yi a shekaru biyu da suka gabata, ya nuna cewa nutsewar da ƙauyen Ravigram ya yi ya kai mita 85 a shekara.
Ana sa rai cewa ministan jihar Uttarakhand, Pushkar Singh Dhami, zai kai ziyara garin Joshimath nan ba da daɗewa ba.