Real Madrid na zawarci Bellingham da Guimares, Barcelona za ta sayar da manyan 'yan wasanta

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta yi nazari kan tsoffin 'yan wasanta irinsu Luka Modric na Croatia mai shekara 37 da Toni Kross mai shekara 33 asalin Jamus kafin ta yanke hukunci kan dauko ɗan wasan Ingila mai bugawa Borussia Dortmund, Jude Bellinghma mai shekaru 19. An shawarci ɗan wasan ya yi watsi da tayin Liverpool. (Diario AS, via Mirror)
Real Madrid na kuma bibbiyar ɗan wasan Newcastle mai shekara 25 asalin Brazil da ke buga tsakiya Bruno Guimaraes a kakar 2022 zuwa 2023 inda ta rasa damarta kan Belligham. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Liverpool na sahun gaba a kokarin cimma yarjejeniya da ɗan wasan Chelsea mai buga tsakiya, Mason Mount a wannan kaka, idan ɗan wasan mai shekaru 24 asalin Ingila ya kasa cimma matsayar sabon kwantiragi a Stamford Bridge. (Mail)
Chelsea ta sake shiga zawacin ɗan wasan RB Leipzig Josko Gvardiol, mai shekara 21, wanda kungiyoyi irinsu Manchester City da Tottenham suka kwadaitu. Dan wasan asalin Croatia sai an biya fam miliyan 97 kamar yada kunshe cikin yarjejeniyar da yake kai a yanzu kafin ya iya sauya sheka daga 2024. (Times - subscription required)
Inter Milan na fatan cimma yarjejeniya da Naby Keita, ɗan shekara 28, a wannan kaka, idan kwantiragin matashin ɗan kasar Guinea ya kare a Liverpool, tuni dai ya soma tattaunawar karfafa masa gwiwa tare da wakilansa.(La Gazzetta dello Sport - in Italian)
Dan wasan Lyon na Faransa Houssem Aouar, mai shekara 24, na dab da cimma yarjejeniya da kungiyar Eintracht Frankfurt bayan watsi da tayin Manchester United. (Sport1, via Mirror)

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona na cikin yanayin da ya zama tilas ta sayar da manyan 'yan wasanta, yayinda kungiyar da ke fama da matsalar tattalin arzikin ke kokarin ganin ta samar da fam miliyan 178. Dan wasan Brazil Raphinha mai shekara 26 na cikin 'yan wasan da babu mamaki a sa shi a kasuwa.(Sun)
Manchester United ta bi sahun Chelsea da Arsenal wajen farautar ɗan wasan Southampton mai shekara 19 Romeo Lavia. (Mail)
Tottenham ta kwaɗaitu da ɗan wasan Bristol City Alex Scott. Matashin mai shekara 19 asalin Ingila na kuma nuna sha'awarsa ga ƙungiyoyin Crystal Palace da West Ham. (Sun)
An shiga tattaunawa tsakanin Manchester United da David de Gea. Mai tsaron ragar daga Sifaniya ɗan shekara 32, ba shi da kungiya tun bayan karewar kwantiraginsa, amma yana son ya cigaba da zama a Old Trafford. (Fabrizio Romano)
Manchester United ta karɓi tayi daga ƙungiyoyin Turkiyya kan ɗan wasanta mai shekara 21 Mason Greenwood, da yanzu haka aka dakatar da shi duk da cewa an wanke shi daga zargin da ake masa na manyan laifuka a watan Fabarairu.(Telegraph)
Napoli na da kwarin gwiwar ci gaba da rike ɗan wasanta Khvicha Kvaratskhelia, mai shekara 22, duk da kwaɗayin da manyan kungiyoyi irinsu Manchester City da Chelsea da Real Madrid da Barcelona ke nunawa. (90min)











