Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wataƙila Sancho ya bar Man Utd, Jamus na neman sabon koci
Ɗan wasan Ingila Jadon Sancho mai shekara 23, na iya barin Manchester United bayan gaza daidaitawa a wata tattaunawa da kocinsa Erik ten Hag, abin da ya kai ga an samu rashin jituwa tsakanin mutanen biyu.(Star)
Manchester United na duba damar iya ɗauko tsohon ɗan wasan Ajax da Aston Villa da ɗan wasan gefe na Everton Anwar El Ghazi, ganin ɗan wasan mai shekara 28 ba shi da wata ƙungiya tun barinsa PSV Eindhoven. (Mail)
Tsohon kocin Bayern Munich Julian Nagelsmann da tsohon kocin Netherlands Louis van Gaal na cikin jeren mutanen da ake son maye gurbin kocin Jamus da aka kora Hansi Flick. (Mirror)
Tauraron Nagelsmann ya fi haskawa a jerin mutanen da ake ganin sun fi dacewa da wannan gurbi, sai dai har yanzu yana cikin yarjejeniya da Bayern Munich, da ka iya neman kuɗi a wajen hukumar ƙwallon kafar Jamus kan kocin mai shekara 36. (Bild)
Tsohon kocin Manchester United Van Gaal ya ce ya ji daɗin shigar da sunansa wannan jerin, sai dai kuma babu wani baƙo da aka taɓa bai wa wannan dama a Jamus. (Sky Sports)
Tsohon kocin Bayern Munich da Fulham Felix Magath na da yaƙinin zai iya zama kocin Jamus saboda kwarewarsa. (Sky Sports)
Manchester United, da ta yi watsi da tayin Arsenal kan mai tsaron raga Mary Earps, ba ta da niyyar sayar da 'yar wasan kafin cikar wa'adin cinikin 'yan wasa a gasar Super Lig ta mata a ranar Alhamis, duk da cewa kwantiragin 'yar wasan mai shekera 30 na karewa a watan Yunin baɗi. (Telegraph)
Chelsea na fargabar sabon ɗan wasanta Romeo Lavia, mai shekara 19, ba zai taka leda ba tsawon mako shida saboda raunin da ya ji a kafarsa a lokacin atisaye. (Mirror)
Hankalin ɗan wasan Arsenal Gabriel ya kwanta bayan shiga fargabar cewa zai iya jin rauni a wasan sada zumunta da tawagarsa ta Brazil ta fafata da Bolivia a ranar Juma'a. (Standard)
Arsenal ta gabatar da tayin fam miliyan 30 kan ɗan wasan Sporting CP Ousmane Diomande, mai shekara 19, wanda aka yi watsi da shi amma ta ce za ta ci gaba da gwada sa'arta kan ɗan wasan n Ivory Coast a baɗi.(Record, Metro)