Isra'ila ta ce sojojinta sun yi kuskure wajen kashe ma'aikatan agaji 15

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Rundunar sojin Isra'ila ta ce gazawar aiki ce ta kai ga kisan ma'aikatan agajin nan 15 a Gaza a watan da ya gabata.

Binciken da rundunar ta yi ta ce ya gano matsaloli da dama da ta ce sun hada da rashin fahimtar aiki, da kuma saba umarni, lamarin da y asa har ta kori wani mataimakin kwamandan sojin nata, kan rawar da ya taka a harin da ta ce an samu kura-kurai.

Kisan ya janyo maganganu da suka daga kasashe da hukumomi na duniya.

A wata sanarwa da ta fitar kan harin, rundunar sojin ta Isra'ila ta lamunta cewa sojojinta su tafka kura-kurai lokacin da suka bude wuta a kan motocin ma'aikatan agajin a Gaza a ranar 23 ga watan Maris da ya gabata.

A harin, sojojin sun kashe ma'aikatan agajin su goma sha hudu da kuma na sha biyar ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya, lokacin harin a kan kwambar motocin agajin da suka kunshi motar majalisar dinkin duniya da wata motar gobara da kuma wasu motocin da daukar marassa lafiya na kungiyar agaji ta Red Crescent.

Rahoton da Isra'ila ta fitar a kan binciken nata ta ce ta kori wani mataimakin kwamandan sojinta saboda rawar da ya taka a harin da ta ce na kuskure, a yankin na Falasdinawa.

Binciken sojin ya ce an samu kura-kurai da dama, amma kuma ya ce, dakarun suna ganin suna fuskantar barazana ne daga mayaka abokan gaba.

Kuma Isra'ilar ta kafe cewa shida daga cikin wadanda aka kashe 'yan Hamas ne tana mai watsi da zargin cewa ta aikata kisan gilla, inda ta ce nan gaba za ta fitar da sunayensu.

Dakta James Smith, wanda likita ne da ke aikin agaji, wanda kuma ya yi aiki a Gaza ya kuma san wadanda aka kashe, ya gay awa BBC cewa binciken na sojin Isra'ila akwai tsumbure a cikinsa:

Ya ce, abin da ake bukata a gaskiya bincike nem ai zaman kansa, ba kawai a kan wannan harin ba, har da daruruwan hare-hare a kan ma'aikatan lafiya da wurare da kayayyakin kula da lafiya tun watan Oktoba na 2023.

Likitan ya kara da cewa Isra'ila na ci gaba da datse hanyar shiga Gaza ga masu bincike masu zaman kansu.

Ya ce ba ta yadda za a yarda dogara ga gwamnatin Isra'ila , ta kasance mai sharia kuma mai bincike a kan saba dokokin duniya da ta yi.

Da farko dai Isra'ila ta yi ikirarin cewa sun bude wuta ne, saboda yadda motocin suka durfafo, a cikin dare, ba fitilu, akwai zargi. Ta ce babu wata masaniya da sojinta suke da a kan zuwan motocin.

Amma kuma daga baya hukumar sojin ta ce, wannan bayani da ta bayar akwai kuskure, bayan da aka gano wani hoton bidiyo a wayar daya daga cikin ma'aikatan agajin da sojin Isra'ilar suka kashe a wannan hari, hoton da ke nuna motocin na tafiya da fitilu a kunne da kuma duk wata alama da za ta fayyace su waye.

Hoton ya nuna yadda motocin suka dakata lokacin da aka fara bude musu wuta, kafin asuba.

Bidiyon ya ci gaba tsawon sama da minti biyar, inda ma'aikacin agajin, yana kalmominsa na karshe, kafin a ji muryoyin sojin Isra'ila sun tunkaro motocin.

An birne gawarwakin ma'aikatan 15 ne kawai a cikin kasa. Kuma ba a tono su ba sai bayan mako daya harin, saboda hukumomin kasa da kasa da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya, ba su iya samun shiga wajen ba ko kuma gano inda abin ya faru.

Haka kuma rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar tana rike da wani ma'aikacin agajin da ta tsare bayan harin.

Ita ma mai magana da yawun kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu, ta ce rahoton, ta ce rahoton na da tasgaro, domin ya saba da gaskiyar ainahin abin da ya faru.