Sojojin Isra'ila sun yi harbi fiye da 100 a kisan ma'aikatan lafiya a Gaza

    • Marubuci, Merlyn Thomas, Emma Pengelly & Matt Murphy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Sojojin Isra'ila sun yi harbi sama da 100 a lokacin da suka kai harin da suka kashe ma'aikatan agaji a Gaza 15, inda wani harbin ma ya kasance kusa da kusa a tazarar da ba ta wuce kafa 39 ba, tsakanin mai harbin da wanda aka harbe, kamar yadda wani sauti da aka naɗa ta waya wanda BBC ta yi nazari a kansa ya nuna.

Wasu ƙwararru a kan sauti sun yi nazari a kan wani hoton bidiyo na tsawon minti 19 wanda BBC ta tabbatar da sahihancinsa - inda bidiyon yake nuna yadda aka kai harin da kuma lokacin da ake shirin kai shi a kusa da Rafah ranar 23 ga watan Maris.

Abin da aka gano ya tabbatar da iƙirarin da ƙungiyar agaji ta Red Crescent da ke yankin Falasɗinawa ta yi cewa, an kai hari kan ma'aikatan ne daga kurkusa.

Sai dai a ranar 5 ga watan Afirilu hukumomin sojin Isra'ila sun ce hoton da aka ɗauka daga sama ya nuna cewa sojojin sun yi harbi ne daga nesa.

Haka kuma rundunar sojin Isra'ila ta ƙi cewa komai a kan sakamakon binciken da BBC ta yi a kan hoton bidiyon lokacin da kafar ta tuntuɓe ta.

Daga baya wani kakakin sojin ya ce suna gudanar da bincike kan harin, amma kuma ya nanata iƙirarin da Isra'ilar ke yi cewa shida daga cikin mutanen suna da alaa da Hamas, amma kuma ba tare da ya bayar da wata sheda ba.

Ƙungiyar Red Crescent ta Falasɗinu ta yi watsi da zargin, kamar yadda wani ma'aikacin lafiya na tara da ya tsira daga harin wanda sojin Isra'ila suka tsare tsawon sa'a 15 ya tabbatar.

Ƙungiyar agajin ta ce an samu cikakken hoton bidiyon ne daga wayar ɗaya daga cikin ma'aikatan lafiyar da sojin Isra'ila suka kashe suka kuma binne a wani dan rami.

Hoton bidiyon wanda ma'aikacin lafiyar Rifaat Radwan, ya ɗauka kafin sojin Isra'ila su kashe shi a harin ya nuna jerin gwanon motoci na tafiya da daddare, fitilun motocin a kunne. Ana iya ganin wani ma'aikacin lafiya sanye da rigar falmaran mai ƙyalli da ma'aikata ke sanyawa domin a hange su a lokacin da suke aiki a wani waje mai haɗari.

Sakamakon wannan bincike da ya bayyana sojojin Isra'ila sun sauya maganar da suka yi a kan yadda suka tunkari wajen lokacin kai harin.

Masu binciken da suka yi nazari a kan bidiyon sun ce an yi harbi na farko ne daga nisan kusan mita 40 zuwa mita 43. Amma kuma a wajen ƙarshen bidiyon an yi harbin daga tazarar mita 12, kamar yadda ƙwararre a kan sauti Robert Maher, na Jami'ar Jihar Montana da kuma wani ƙwararren Steven Beck suka tabbatar a nazarin da suka yi daban-daban.

Wani tsohon sojan Birtaniya, da ya yi shekara 20 a aiki, Chris Cobb-Smith, wanda kuma ya ƙware wajen gudanar da bincike a yankunan da ake rikici ya ce daga tazarar mita 50 kaɗai sojojin Isra'ila za su iya gane cewa tawagar motocin da suka buɗe wa wuta ta masu aikin agaji ce - wadda ba ta ɗauke da makamai ko kuma wata barazana.

"Tashi tsaye," da kuma: "Ku koma baya".

Masu binciken sun ce a wani lokacin ma an shafe sama da minti biyar ana harbi ba ƙakƙautawa.

Mista Maher ya ce, "ana iya jin ƙarar harbin wani na shiga wani - wanda hakan ya tabbatar ƙarara cewa an buɗe wuta ne kawai a wajen a lokaci ɗaya.

Mai nazarin ya ce saboda ƙaran wata bindigar na shiga na wata abu ne mai wuya a iya gane, harbin wani mutum ɗaya . To amma dai ƙwararrun biyu a nazarin da suka yi daban-daban sun tabbatar da cewa an yi harbin da ya fi 100 a lokacin.

Ƙwararrun da suka yi wa BBC nazarin sautin ba su ce komai ba a kan irin makaman da aka yi amfani da su ba a harin amma, Mista Beck akwai ƙaran harbi da dama na bindiga mai sarrafa kanta.

Yadda ƙwararru suka yi nazarin sautin

Harsashin da yake gudu da sauri kamar na walƙiya da farko zai yi wani sauti na daban. Kuma lokacin da aka harba harsashin ƙaran ya bambanta da na lokacin da yake gudu.

Idan a kusa ne aka yi harbin kunnen mutum ba zai iya tantance ƙaran biyu ba.

To amma idan aka kalli hoton igiyar sautin a na'ura za a iya bambance sautin biyu, har ma a iya auna tazarar da ke tsakaninsu.

Ta haka ne Mista Maher ya ce, ana iya ganin wannan bambanci a nazarin hoton ƙaran da aka yi a na'ura.

Mista Maher, ya ce idan bindigar ta kasance ta yi ɗan nisa daga wayar da ke naɗar sautin, za a iya ganin tazarar a tsakanin hotunan igiyar sautin biyu a na'ura.

Ba komai ba ne binciken ƙwararrun ya iya ganowa a wannan nazari da suka yi kan bidiyon harin, kamar yadda suka sheda wa BBC cewa ba su da tabbaci a kan irin bindigar da aka yi amfani da ita ko kuma tazarar mai harbin da kuma wanda aka hara da harbin. Haka shi ma gudun harsashin sun yi hasashe ne a kai.

BBC za ta ci gaba da gudanar da bincike a kan wannan lamari.