Tottenham ta sallama tayin da Leicester ta yi wa Skipp

Oliver Skipp

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tottenham ta sallama tayin da Leicester City ta yi wa Oliver Skipp.

An ce ƙudin da aka taya mai shekara 23, wanda ya fara daga makarantar horar da tamaula ta ƙungiyar ya kai £20m.

Ana sa ran ranar Litinin Skipp zai je a auna koshin lafiyarsa a King Power, kafin wasan makon farko a Premier League da za su fafata.

Ɗan wasan tawagar Ingila ta matasa ƴan kasa da shekara 21 ya fara yi wa Tottenham tamaula a Oktoban 2018.

Kawo yanzu ya buga mata karawa 77 a Premier League har da fafatawa 21 a bara, inda Tottenham ta kare a mataki na biyar a teburi.

Skipp zai je ya taka leda tare da tsohon ɗan wasan Tottenham, Harry Winks, kenan Skipp zai zama na biyar da Leicester ta ɗauka kan fara kakar bana.

Leister City ta samu gurbin shiga babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana, bayan da ta lashe Championship a bara.