Garkuwan Yahaya ya buge Ushu Shagon Inda a Maraba

An wallafa

Ushu Shagon Inda ya yi rashin nasara a hannun Garkuwan Yahayan Tarasa a damben safiyar Lahadi a Marabar Nƴanya a jihar Nasarawa, Najeriya.

Sun dambata ne a ajon Labaran dan gwamba, makadin ƴan dambe da aka yi masa a ƴan tifa da ke karamar hukumar Karo.

Tun farko Wazirin Labaran ɗan Gwamba ne ya hada dambe, bayan da ya fara kiran Garkuwan Yahaya, sannan ya kira Ushu gabansa, wadanda suka amince da haɗin.

Bayan da fili ya nutsa ne sai suka shiga cikin filin wasa, inda alkalin wasa Anas ɗan Dume ya daga hannunsu da cewar sune a kan lafi.

Nan da nan aka sa zare tsakanin Garkuwan Yahaya Guramaɗa da Ushu Shagon Inda daga Arewa.

Cikin turmin farko da suka fara wasan kai sai ka za ta babu abin bajinta da za a yi a dambe, amma kan lokaci ya ja Garkuwan Yahaya ya kai bugu da mangare ya kuma samu Ushu da ta kai ya kai kasa, amma da kansa ya tashi.

Daga nan makada suka zagaya da ɗan damben Guramaɗa cikin ƴan kallo, inda masoya suka yi ta yi masa alheri.

To sai dai ba a samu damar buga damben gasa ba tsakanin Ɗan Aliyu da Autan na Aisha ba, watakila mako mai zuwa su sa zare a tsakaninsu.

Wasannin da aka yi kisa:

  • Shagon Shamsu ya buge Dogon VIO
  • Garkuwan Duna ya buge Garkuwan Isa
  • Sabon Gundumi ya sumar da Shagon ɗan Aliyu
  • Mabilu ya sumar da Shagon Lagada

Damben da mai yi kisa ba:

  • Shagon Terminator da Lagada
  • Amir Shagon Inda da Shagon na Jimama
  • Shagon Autan ɗan Bunza da Sabon Gundumi
  • Shagon Ƴansanda da Ilele
  • Dogon Inda da Bahagon Yahaya
  • Shagon Shamsu da Shagon Terminator
  • Aljanin Nokiya da Sabon Gundumi
  • Lagada da Shagon Na Maleka