Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saka ya ce a shirye yake ya buga dukkan wasannin Arsenal
Bukayo Saka ya ce a shirye yake ya buga wa Arsenal wasa 70 a kakar nan, duk da ana cewar jikinsa ba zai iya ɗauka ba.
Ɗan Ƙwallon tawagar Ingila, mai shekara 22, shi ne ya yi kyaftin ranar Asabar da Arsenal ta doke Sheffield United 5-0 a gasar Premier League.
Hakan ya sa Arsenal tana ta biyun teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki biyu tsakaninta da Tottenham ta ɗaya.
Saka ya yi wa Gunners dukkan karawar da ta yi a kakar nan, in banda wasa ɗaya a Premier League da kuma ɗaya a Champions League.
Bai buga karawar da Arsenal ta ci Manchester City ba a Emirates, hakan ya kawo ƙarshen wasa 87 a jere tun daga Mayun 2021 a Premier League.
Ƙwazon da Saka ke yi a wasanninsa na ƙara ƙarfin Gunners, hakan ya sa Mikel Arteta ya yi kira ga dan wasan ya ci gaba da sa ƙwazo, domin su lashe kofuna.
Saka, wanda ya yi wasa 62 a bara a tawagar Ingila da Arsenal, ya ce zai ci gaba da kokarin da Arteta ke bukata, domin kai kungiyar ga nasarori.
''Ina jin abu ne mai yiwuwa,'' in ji Saka. ''Idan ka kalli fitattun 'yan kwallo kullum suuna kan ganiya a wasa dasuke duk bayan kwana uku da laushe kyautuka ga kungiyoyinsu.''
''Saboda haka nima abin da na ke son cimmawa kenan, zan ci gaba da sa kwazo, koda yake da kalubale, amma zan ci gaba da mayar da hankali yadda ya kamata.''
Ana sa ran watakila Arteta ya hutar da Saka ranar Laraba a Caraboa Cup da West Ham United zagaye na hudu.
Sai dai ana sa ran zai kara yin kyaftin a fafatawar da Arsenal za ta ziyarci Newcastle United a St James Park ranar Asabar a Premier League.
Martin Odegaard na jinya tare da Gabriel Jesus.