Aikin koci a Premier zai iya shafar lafiyar kwakwalwa in ji Potter

Graham Potter

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Graham Potter ya ce aikin horar da tamaula a Premier League na tattare da kalubalen da zai iya shafar lafiyar kwakwalwa.

Kociyan wanda ke jimamin mutuwar mahaifansa na fama da kalubalen yadda zai komar da Chelsea kan ganiya.

Mai shekara 47 ya maye gurbin Thomas Tuchel a watan jiya a Stamford Bridge, bayan da dan kasar Jamus ya kasa taka rawar gani a kakar nan.

A wasan farko Tuchel ya yi 1-1 da RB Salzburg a Champions League daga nan ya ja ragamar wasa takwas ba a doke Chelsea ba.

Tsohon kociyan Brighton ya ci wasa shida da canjaras uku tun bayan da ya karbi aikin horar da Chelsea ranar 8 ga watan Satumbar 2022.

A lokacin da cutar korona ta yi kamari ne mahaifiyar Portter ta mutu, sannan wata shida tsakani, shima babansa ya bar duniya.

A kuma lokacin tsohon mai tsaron bayan Birmingham da Stoke da kuma York na aikin horar da Brighton a Premier League.

Da yake yanzu yana aiki da Chelsea ya ce idan za ake kwatanta shi da wanda ya gada a Chelsea ko wannan zai iya shafar lafiyar kwakwalwa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''Kafin na koma Brighton bani da kwarewar horar da tamaula a Premier League, saboda haka na koyi yadda ya kamata na gudanar da aikin.''

Ya fadi haka ne don amsa tambayar da aka yi masa kan babban darasin da ya samu a kaka uku da ya yi a Brighton.

''Wasu lokutan sai ka sha wuya, sannan ka samu kwarewa cikin dan karen radadi, sannan yayin da kake kara yin sama a Premier League haka surutai zai karu.

''Kafofin yada labarai na son hada kwazo na da Thomas Tuchel abin da ke faruwa a yanzu haka kenan. Wanda hakan ba abu bane mai dadi, domin zai iya shafar lafiyar kwakwalwa.''

Potter wanda ya ja ragamr Brighton wasa 135 da cin karawa 42 da canjaras 46 da rashin nasara 47, ya kai kungiyar mataki na tara a bara, shi ne kololuwar da ta taba yi a gasar.

Potter ya kara da cewar ''Kowanne wasa a Premier na hamayya ne mai cike da kalubale, koda yaushe sa rai ake sai ka yi nasara, bayan dole wata ran za a doke ka.

''Kana fama da zabar 'yan kwallon da za su buga maka wasa, bayan Premier ga Champions League ga FA ga League Cup, sai ka kula da 'yan wasan da ke kan ganiya.''

''Kungiyoyi yanzu ba hakuri kowa sakamako mai kyau yake bukata, sannan magoya baya kan sa matsi ga koci da zarar wasa ya juya baya.''

Yanzu dai Chelsea na taka rawar gani a wasanninta, wadda ta kai zagayen gaba a Champions League, tana kuma ta biyar a teburin Premier League.

Potter zai kara da Brighton a gasar Premier League ranar Asabar, karon farko tun bayan da ya bar kungiyar da ya ja ragama kaka uku.

Wasannin Premier League na mako na 12:

Asabar 29 ga watan Oktoba

  • Leicester City da Manchester City
  • Newcastle United da Aston Villa   
  • Crystal Palace da Southampton    
  • Bournemouth  da Tottenham
  • Brighton da Chelsea       
  • Brentford da Wolverhampton
  • Fulham da Everton  Match details
  • Liverpool da Leeds United