Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ta kwace teburin Premier daga wajen Arsenal
Manchester City ta doke Arsenal 3-1 a Emirates a kwantan wasan mako na 12 a gasar Premier League ranar Laraba.
Minti 24 da fara wasa Kevin de Bruyne ya fara cin kwallo, daf da za a je hutu Arsenal ta farke ta hannun Bukayo Saka.
Jack Grealish ne ya ci wa City na biyu, sannan Erling Haaland ya kara na uku da hakan kungiyar Etihad ta hada maki ukun da take bukata.
Kwallo na 26 da Haaland ya zura a raga a bana a Premier League ya yi kan-kan-kan da yawan na Sergio Aguero a City a kakar 2014/15.
Da wannan sakamakon Manchester City ta koma ta daya a kan teburi da maki 51 iri daya da na Arsenal wadda ta yi kasa zuwa ta biyu da tazarar rarar kwallaye.
Gunners wadda ke fatan lashe Premier a karon farko bayan kaka 19 ta ci karo da koma baya kwanan nan, wadda Everton ta doke ta 1-0 da yin 1-1 da Brentford ranar Asabar.
City wadda ita ta fitar da Arsenal daga FA Cup a bana da cin 1-0 ta casa Aston Villa 3-1 ranar Lahadi a Premier League.
Pep Guardiola ya dauki Premier League hudu tun bayan da ya karbi aikin jan ragamar City a 2016
Mikel Arteta tsohon dan wasan Gunners ya koma aikin horar da Arsenal daga City a matakin mataimakin Guardiola.
Arsenal ta yi rashin nasara a wasa 11 a jere a hannun Manchester City - kungiyar da ta ci Gunners a karawa da yawa a jere a tarihin gasar kenan.
City ta yi nasara a wasa na bakwai baya da ta ziyarci Arsenal a dukkan fafatawa.
Kungiyar Etihad ta zama ta farko da ta ci Arsenal sau bakwai a jere a gida a Premier League.
Rabon da Gunners ta doke mai rike da Premier League tun 1-0 da ta yi nasara a kan Leicester City a Afirilun 2017.
Manchester City ce kadai da Arteta bai ci ba a matakinsa na kociyan Premier League - ya yi rashin nasara shida a karawa da City da cin kwallo biyu aka zura masa 15.
Wasa na 23 da City ta lashe a Premier League da take buga wa ranar Laraba.
City ta ci dukkan wasa 22 da ta yi a Premier League ranar Laraba, ba wadda ta yi wannan kwazon.