Ƴadda aka tilasta wa wasu ƴan Kenya amfani da 'soyayya' su aikata zamba

An wallafa

Daga cikin wasiƙun da muke samu daga yan jarida na nahiyar Afrika, Waihiga Mwaura daga gidan talabijin na Citizen TV daga Kenya ya duba mana yadda masu safarar mutane ke damfarar ƴan ƙasar Kenya da sunan masu ɗaukar aiki.

Duk abin da ya fi kyau da ɗaukar ido, watakila ba gaskiya bane. Wannan shi ne saƙon da ma'aikatar harkokin waje ta Kenya ke aikawa domin ta gargaɗi masu neman aiki waɗanda aka ja hankalinsu ta hanyar samun aiki a kudu maso gabashin nahiyar Asia.

Wannan na zuwa ne bayan ceto sama da ƴan ƙasar Kenya 60 daga ƙasar Myanmar da Laos a watannin da suka gabata - bayan ayyukan da mutanen suka nema a Thailand a matsayin masu sayar da kayayyaki ko aikin kula da kwastamomi ya kasance ashe ayyuka ne na laifuka ta intanet da karuwanci da sayar da gaɓoɓin bil adama.

"Tuni wani matashi daga Kenya ya rasu sakamakon wata tiyatar ganganci da wani jabun likita ya yi masa a wani kamfanin ƴan China a Myanmar," kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen ta Kenya ta tabbatar a makon da ya gabata.

Na yi magana da wasu mata biyu kan yadda suka ji. Sun buƙaci a sakaya sunansu, wata mai shekara 31 wadda ke da shaidar karatu ta Difloma kan kula da otel, da kuma wata mai shekara 35 wadda ta kammala sakandire sun shaida mani yadda suka tafi Thailand aiki a watan Agusta inda aka yi musu alƙawarin dala 800 a duk wata.

Wata guda kafin tafiyarsu, dukansu sun ranci kusan dala dubu biyu domin biyan agent ɗin su domin tafiya da kuma zuwa wani horo na musamman.

A lokacin da suka isa Thailand, waɗanda za su karɓe su sai suka yi tafiya mai tsawo da su kan titi inda suka tsallaka da su kusan kowane kogi zuwa ƙasar Laos mai maƙwaftaka

A ƙarshe sai aka kai su wani gini mai hawa 15, wanda ya kasance gidansu na din-din-din - duk da ba su san wani gari ko birni aka kai su ba.

Sai a nan ne suka fahimci cewa a maimakon aikin kula da kwastamomi, an kai su can ne domin aikata laifuka ta intanet - ciki har da neman ƴan Amurka ta hanyar buɗe shafi mai jan hankali a manhajojin Tinder da Instagram da Facebook.

"Za su soma soyayya da mutum sai mutum ya soma musu maganar kuɗin crypto. Sai mu soma musu sata," kamar yadda matar mai shekara 31 ta shaida, inda ta bayyana a harshen Swahili kan yadda dukansu aka tilasta musu yin aiki a wani katafaren wuri mai kama da ɗakin taro wanda yake ɗauke da ɗaruruwan mutane daga ƙasashe daban-daban.

Babu wanda a cikinsu ya karɓi albashin da aka yi masa alƙwari inda a maimakon haka aka rinƙa yi musu barazana da aikin karuwanci ko kuma cire wani sashen jikinsu domin sayar da su su mayar da kuɗin da suka kashe wurin kawo su," kamar yadda ta bayyana.

"Sun shaida mana: 'Dole ku biya kudin Kenya miliyan 1.2 (dala 10,000) domin ku ceci kanku domin mu ke da ku."

Kamfanonin damfara

Sai matan biyu suka samu sa'ar tuntubar ƙungiyar yaƙi da safarar bil adama ta Awareness Against Human Trafficking ta intanet, wadda ƙungiya ce a ƙasar Kenya da ke taimakon yan ci rani da suka shiga tasku, inda daga baya aka ceto su aka kuma dawo da su gida ta taimakon hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya da Kenya.

Labarinsu ya yi kama da na wasu ƴan Kenya waɗanda aka ajiye su a wani wuri da ma'aikatar harkokin wajen Kenya ta kira "kamfanonin damafara" da kuma "sansanin aikin bauta" inda "ake ƙwace fasfon su ya zama ƙarƙashin kulawar gungun masu laifin".

Hukumar ta bayyana cewa duk da akwai agent-agent da dama na ɗaukar aikin da ƴan sanda ke nema ruwa a jallo, amma duk da haka suna ci gaba da tallata ayyukan da babu su a ƙasa a Thailand inda mutanen Kenya suka ci gaba da faɗawa tarkonsu.

"Wani samame da sojoji suka kai ya yi sanadin rasuwar sama da mutum 60 a wani wuri da ƴan tawaye ke da iko da shi, waɗanda suka bayar da tsaro ga gungun ƴan China," kamar yadda ma'aikatar ta Kenya ta yi gargaɗi.

Jumullar mutum 76, ciki har da ƴan Uganda 10 da ɗan Burundi ɗaya aka tasa ƙeyarsu tun a watan Agusta da taimakon jami'ai a ofishin jakdancin Kenya da ke Thailand.

Matasan ƴan Afrika masu ilimi ne gungun ke hari domin suna ganin su ne za su iya aikata laifukan ta intanet.

Duk wannan na nuni ne da tsananin rashin aikin yi a nahiyar da kuma yadda gwamnatocin da suka samu dama suka yi alƙawuran ayyukan yi.