Rangers ta sayi Ben Davies daga Liverpool

An wallafa

Rangers ta amince za ta sayi mai tsaron baya, Ben Davies kan fam miliyan hudu daga Liverpool.

Davies ya koma Liverpool da taka leda daga Preston kan fam 500,000 a Fabrairun 2021 lokacin da 'yan wasan kungiyar da yawa ke jinya.

'Yan kwallon Liverpool da dama sun yi ta yawan rauni musamman gurbin masu tsaron baya daga tsakiya.

Liverpool ba ta fara wasa da shi a kakar da ta wuce ba, wadda ta bayar da aronsa ga Sheffield United.

Rangers ta sayi Davies, bayan da ta amince za ta sayar da Calvin Bassey ga Ajax, wadda ta sallamar da dan kwallon Najeriya kan fam miliyan 20.