Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
''Ya kamata a daina yi wa Neymar keta'' kociyan Brazil
Kociyan Brazil, Tite ya ce ya kamata a kawo karshen yawan yi wa Neymar keta a tamaula, bayan da dan wasan ya ji rauni a karawa da Serbia.
An nuna Neymar a kan benci yana kuka, bayan da aka sauya shi a minti na 80, sakamakon raunin da ya ji.
Mai shekara 30 ya ji rauni ne, sakamakon ketar da Nikola Milenkovic ya yi masa a wasan da Brazil ta ci 2-0 ranar Alhamis.
Tun da ya fara buga Gasar Kofin Duniya a 2014 an yi wa Neymar keta 53, kenan a kalla sau 11 fiye da kowanne dan wasa.
A fafatawa da Serbia an yi masa keta sau tara fiye da kowa a fafatawar ta farko a rukuni na takwas.
Kenan Neymar ba zai buga sauran wasa biyu na rukunin ba, sai dai Tite na fatan Neymar zai buga wa Brazil karawar zagaye na biyu a Qatar.
Ranar Litinin Brazil za ta kara da Switzerland a wasa na biyu a rukuni na takwas, sai dai Danilo shima yana jinya, wanda ya ji rauni a wasa da Serbia.
Haka watakila dan wasan Switzerland, Renato Steffen bai zai yi wasan ba, saboda bai murmure ba.
Abin da ya kamata ku sani kan wasan Brazil da Switzerland
Wasa biyu baya da suka tashi a kofin duniya sun raba maki a 1950 suka tashi 2-2 da 1-1 a 2018.
Brazil ta yi karawa 16 a cikin rukuni ba tare da an doke ta ba a Gasar Kofin Duniya, ba kasar da ta yi fafatawa 17 ba a doke ta ba.
Switzerland na fatan cin wasa biyu a jere a Gasar Kofin Duniya a karon farko a tarihi.
Richarlison ya ci wa Brazil kwallo tara a fafatawa bakwai baya da ya yi mata a dukkan fafatawa.
Breel Embolo ya ci kwallo uku a karawa hudu da ya yi wa Switzerland.