Liverpool ta tsawaita kwantiragin Diago Jota

Diago Jota

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Dan kwallon Liverpool, Diogo Jota ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa karshen kakar 2027.

Dan wasan tawagar Portugal, mai shekara 25 ya ci kwallo 34 a karawa 85, tun bayan da ya koma kungiyar daga Wolverhampton a 2020 kan fan miliyan 41.

Ya ci kwallo 21 a bara da Liverpool ta dauki FA da Caraboa Cup da yin ta biyu a Premier League da Champions League.

Jota, wadda yarjejeniyarsa tun farko za ta kare a 2025, bai buga wa Liverpool wasannin sada zumunta don tunkarar kakar bana, sakamakon jinya.

A watan jiya Mohamed Salah ya saka hannu kan kwantiragin ci gaba da zama a Liverpool kaka uku, bayan da Sadio Mane ya koma Bayern Munich a bana.