Euro 2024: Ingila ta doke Slovekia ta kai kwata fainal

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Ingila ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe, bayan da ta doke Slovekia da cin 2-1 ranar Lahadi a Euro 2024.
Slovekia ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Ivan Schranz a minti na 25 da take leda, kuma haka suka je hutu da wannan sakamakon.
Sai daf da za a tashi ne Ingila ta farke ƙwallon ta hannun Jude Bellingham, wanda ke bikin ranar haihuwarsa.
Tsohon ɗan wasan Borussia Dortmund, mai taka leda a Real Madrid an haife shi ranar 30 ga watan Yunin 2003, kenan yana da shekara 21 da haihuwa.
Daga baya ne ƙyaftin din tawagar Ingila, Harry Kane ya kara na biyu, bayan karin lokaci da suka yi minti 120 suna barje gumi.
Da wannan sakamakon Ingila za ta buga daf da na kusa da na karshe da Switzerland ranar 6 ga watan Yuli.
Ranar Asabar Switzerland ta fitar da mai rike da kofin Italiya da cin 2-0 a karawar zagaye na biyu.
Wannan shi ne wasa na 99 da kociyan Ingila, Gareth Southgate ya ja ragamar tawagar.
Ya fara aiki da cin Malta 2-0 a karawar neman shiga gasar cin kofin duniya cikin Oktoban 2016.
Kobbie Mainoo ya maye gurbin Conor Gallagher a wasa da Slovekia
Gareth Southgate ya yi sauyin ɗan wasa ɗaya a karawar da ya doke Slovekia daga 11 da ya fuskanci Slovenia a fafatawar cikin rukuni na uku a Euro 2024.
An sa ɗan wasan Manchester United, Kobbie Mainoo ya maye gurbin na Chelse, Conor Gallagher - wanda ya ji rauni a karawa da Slovenia.
Ƴan wasan Ingila 11: Pickford da Walker da Stones da Guehi da Trippier da Mainoo da Rice da Saka da Bellingham da Foden da kuma Kane.
Masu zaman benci: Ramsdale da Henderson da Shaw da Alexander-Arnold da Konsa da Dunk da Gallagher da Toney da Gordon da Watkins da Bowen da Eze da Gomez da Palmer da kuma Wharton.










