Real Madrid na harin Calafiori, Tottenham na son Romero

Asalin hoton, AFP
Real Madrid na son ganin ta siyo ɗan wasan Arsenal da Italiya Riccardo Calafiori, da ya taka leda a hannun Jose Mourinho a Roma. (Sky Sports)
Tottenham na duba yiwuwar siyo dan wasan Juventus da Brazil Gleison Bremer, don maye gurbin dan wasan ƙungiyar Cristian Romero, da kuma ƙara inganta tsaron bayan kungiyar. (Tuttosport - in Italian)
Manchester United ba su da ra'ayin ɗauko Romero daga Tottenham , amma suna son ɗaukar ɗan wasan Newcastle Lewis Hall. (Teamtalk)
Daya daga cikin mamallakan ƙungiyar Sir Jim Ratcliffe na son amincewa da buƙatar ɗan wasan Nottengham Forest Elliot Anderson domin ganin sun kawo shi Manchester United. (Mirror)
Manchester City ce kan gaba cikin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar Anderson duk da yunƙurin United na ganin sun shammace ta wajen siye ɗan wasan. (Star - subscription required)
Sabon mai horar da ƴan wasan Real Madrid Jose Mourinho na harin ɗan wasan West Ham Mateus Fernandes da ke son komawa Chelsea. (AS - in Spanish)
Manchester United har ila yau na duba yiwuwar siyar da Fernandes ga West Ham, kan Fam miliyan 80, sai dai United din ba gaggawa suke ba wajen siyar da Fernandes . (Sky Sports)
Manchester United na duba yiwuwar bayar da wani mamaki na ɗauko mai tsaron ragar Leeds Karl Darlow, da kwantaraginsa ta ƙare da ƙungiyar, a wannan kaka, yayin da mai tsaron ragar United ɗin ke shuirin barin Old trafford ɗin. (Talksport)
Fulham na harin ɗan wasan Najeriya Samuel Chukwueze daga AC Milan sakamakon tsawon lokacin da ya dauka a mastyin ɗan wasan Aro a Craven Cottage, sai dai suna ci gaba da tattaunawa wajen biyan kuɗi kaɗan. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Atletico Madrid na sa ran siyen ɗan wasan Manchester City Bernando Silva maimakon Barcelona ko Real Madirid saboda za su iya bai wa ɗan wasan na Portugal isasshen lokacin taka leda. (Marca - in Spanish)
Fulham na duba yiwuwar ɗauko mai hororar da ƴan wasan Ipswich Kieran McKenna, wanda ke kan gaba a jerin waɗan da suke son ɗauka don maye gurbin Marco Silva. (Talksport)
Leicester na tattaunawa da tsohuwar ƙungiyar mai horar da ƴan wasan Southampton da Rangers Russell Martin kan yiwuwar komawarsa ƙungiyar sakamakon rasa gurbin buga Firimiya, inda suka koma buga League One. (Leicester Mercury)














