Abin da BBC ta gano lokacin da ta shiga Asibitin Al-Shifa na Gaza

BBC correspondent Lucy Williamson walks inside the compound of Al-Shifa Hospital, in Gaza City, during an operation by the Israel Defense Forces (15 November 2023)
Bayanan hoto, Dakarun Isra'ila sun ƙayyade iya wurin da BBC za ta shiga a Asibitin Al-Shifa kuma ba a bari tawagar ta yi magana da likitoci ko masu jinya ba
    • Marubuci, By Lucy Williamson at Al-Shifa hospital, Gaza City
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Mun lallaɓa zuwa cikin farfajiyar Asibitin Al-Shifa cikin duhu ta kusa da wani garu da aka rusa da buldoza ranar Talata don bai wa dakarun Isra'ila damar shiga.

BBC da wata kafar talabijin ne 'yan jarida na farko da dakarun Isra'ila (IDF) suka gayyata don ganin abin da suka ce sun gano a wurin game da mayaƙan Hamas.

Duk wani ƙarin haske da muka haska a nan abin haɗari ne, a haka muka yi ta kurɗawa cikin asibitin bisa rakiyar dakaru masu ɗauke da manyan makamai, inda muka dinga tsallake tantuna, da ɓaraguzai, da mutane kwance suna barci.

Likitocin asibitin sun ce sun yi ta aiki ba tare da lantarki ba, ko abinci ko ruwa tsawon kwanaki - kuma sakamakon haka masu jinya sun rasu, cikinsu har da jarirai.

Ga kuma dubban mutanen da ke fakewa a asibitin bayan an rusa gidajensu sakamakon hare-haren Isra'ila a faɗin Zirin Gaza.

Laftanar Kanar Jonathan Conricus ya nuna wa tawagar BBC wani ɓangare na Asibitin Al-Shifa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Laftanar Kanar Jonathan Conricus ya nuna wa tawagar BBC wani ɓangare na Asibitin Al-Shifa

Sai dai Isra'ila na cewa Hamas na da hanyoyin ƙarƙashin ƙasa a ƙarƙashin asibitin na Al-Shifa.

Dakaru na musamman da ke yi mana rakiya sun rufe fuskokinsu, abin da ke nuna irin yanayin da ake ciki a nan.

A sashen ɗaukar hoto na MRI, Kanar Conricus ya nuna mana ƙunshin bindigogi uku , da harsasai, da rigunan kariya - ya ce sun gano bindigogi kusan 15 jimilla tare da gurneti.

Ya kuma nuna mana wasu takardun soji, da tasawira da ya ce suna ƙunshe hanyoyin shiga da fita daga asibitin.

Sojojin Isra'ila sun ce sun gano bindigogi ƙirar Kalashnikov a cikin na'urar ɗaukar hoton cuta ta MRI a Asibitin Al-Shifa
Bayanan hoto, Sojojin Isra'ila sun ce sun gano bindigogi ƙirar Kalashnikov a cikin na'urar ɗaukar hoton cuta ta MRI a Asibitin Al-Shifa
A pamphlet entitled “Military Ordnance” published by the Palestinian Authority, and another pamphlet (underneath) published by the Izzedine al-Qassam Brigades, Hamas’s military wing, which Israel Defense Forces (IDF) soldiers said they found inside Al-Shifa Hospital in Gaza City (15 November 2023)

Abin da haka ke nufi, a cewarsa, Hamas na amfani da asibitoci a matsayin wuraren yaƙi. "Kuma mun gano kwamfutoci da yawa da sauran kayan aiki da za su iya ba mu ƙarin bayani game da halin da ake ciki, musamman game da mutanen da ake garkuwa da su."

Kwamfutocin na tafi-da-gidanka, in ji shi, na ɗauke da hotuna da bidiyoyi, waɗanda aka ɗauka bayan sace su zuwa Gaza. Sai dai ba a nuna wa BBC abubuwan da ke cikinsu ba.

A cewarsa, hakan ya nuna "mayaƙan Hamas na asibitin 'yan kwanaki da suka wuce".

"A ƙarshe dai wannan somin-taɓi ne," in ji shi. "Hamas ba su gudu daga nan ba saboda sun ga muna shirin zuwa. Ƙila dai abin da suka iya bari ke nan a nan. Amma hasashenmu shi ne akwai ƙarin wasu sosai."

A building at Al-Shifa Hospital in Gaza City during an operation by Israel Defense Forces soldiers (15 November 2023)
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sojin Isra'ila sun shafe makonni suna fafatawa kafin su iya kaiwa ga ƙofar asibitin. Titunan da ke kusa sun fuskanci ƙazamin faɗa mafi girma a Gaza.

An ƙayyade abin da za mu iya yi a ziyarar sosai; an ba mu 'yan mintuna kaɗan kuma ba a ba mu damar yin magana da likita ko maras lafiya ba.

Ita kanta balaguron da muka yi zuwa cikin Birnin Gaza, mun yi ta ne cikin motar silke wadda babu abin da ake iya gani ta waje sai duhu, amma hanyar na nuna hare-haren Isra'ila ta ƙasa da suka fara kaiwa makonni da suka gabata.

Muna iya hangen yadda gonaki masu amfani a cikinsu ke sauyawa a hankali zuwa masu cike da ɓaraguzai, ga kuma titunan da manyan ƙarafan gini suka mamaye.

Mun tsaya a kudancin Gaza don sauya mota, inda muka lallaɓa ta tsakanin ƙarafa da ɓaraguzan da suka shafe hanya.

Wani ɗan gungun sojoji sun zagaye wata wuta da suka kunna suna girki a kusa da tankokin yaƙi.

A sama da su kuma, gine-gine ne masu wata kama ta musamman - sakamakon hare-haren Isra'ila ta sama.

An zana Tauraruwar David a jikin wani bango da jan fanti; a cikinta wani ya rubuta "IDF", a samanta kuma: "Ba Za a Sake Maimaitawa Ba".

A Star of David spray-painted on a wall south of Gaza City, with the word "IDF" written inside it, and above it, the words: "Never Again"

Harin ranar 7 ga watan Oktoba ya sauya lissafin Isra'ila a rikicin da take yi da Hamas. Ta ci alwashin kawo ƙarshen hatsaniyar ta hanyar tarwatsa ikon soji da siyasar Hamas, ƙungiyar da Amurka da Birtaniya da wasu ke kallo a matsayin ta 'yan ta'adda.

Hakan na nufin kutsawa cikin Birnin Gaza, da kuma Asibitin Al-Shifa.

Har yanzu sojojin Isra'ila na bincika inda hanyoyin ƙarƙashin ƙasar suke a asibitin, waɗanda ta ce Hamas na riƙe da mutanen da take garkuwa da su a cikinsu.

Wannan ginin ya zama babbar alƙiblar yaƙin Isra'ila, wanda ta bayyana da cewa babbar cibiyar Hamas, ko kuma ma "zuciyar yaƙi" ta ayyukan Hamas ɗin.

Sojojin Isra'ila sun shafe makonni kafin su iya zuwa asibitin da ke tsakiyar Birnin Gaza. Sannan a irin wannan lokaci na yaƙi a fannin yaɗa labarai, wannan ne lokaci mafi muhimmanci ga Isra'ila na nemo hujja.

Bayan kusan awa 24 suna duddubawa da kuma ba da tsawo a asibitin, Isra'ila ta ce ta gano makamai da sauran kayayyaki da za su taimakawa wajen bayar da bayanai kan Hamas da kuma mutanen da take garkuwa da su. Zuwa yanzu dai ba ta samu ko ɗaya daga ciki ba.

Mun bar asibitin, inda muka nufi titin da zai zarce zuwa gaɓar ruwa. Yanzu dai tankunan yaƙi ne ke mulkin Gaza. Ɓarnar da aka yi a birnin ta fi kama da irin abin da aka saba gani a wuraren da aka yi girgizar ƙasa saboda girmanta.

A bayyane take irin ɓarnar da hare-haren Isra'ila suka yi kafin sojoji su iya samun iko da titunan birnin.