West Ham ta doke United gida da waje a Premier League a bana

Amorim

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta yi rashin nasara 2-0 a hannun West Ham United a Old Trafford a wasan mako na 36 a Premier League ranar Lahadi.

Tomas Soucek ne ya fara cin ƙwallo a minti na 26 da fara wasan, sannan Jarrod Bowen ya kara na biyu a zagaye na biyu a fafatawar.

West Ham ta yi nasara a kan United 2-1 cikin watan Oktoba a wasan farko a kakar nan, inda Crysencio Summerville da Jarrod Bowen suka ci mata ƙwallayen.

Ita kuwa United ta zare ɗaya ta hannun Casemiro, saura minti tara a tashi daga fafatawar a gidan West Ham.

Wannan shi ne karon farko da West Ham ta yi nasara a kan United gida da waje a Premier League a kakar tamaula tun bayan 2006/07.

Kawo yanzu United ta yi wasa bakwai ba tare da yin nasara ba, da yin canjaras biyu daga ciki, karo na biyu da ta yi haka, bayan tsakanin Satumba zuwa Nuwambar 1992.

Karo na 17 da aka ci Man United a kakar nan a Premier League, ƙwazo mafi muni tun bayan 1989/90.

West Ham ta haye mataki na 15 da United take kai a baya, ta kuma haɗa maki 40, saura wasa biyu ya rage mata.

Ita kuwa United ta yi kasa zuwa mataki na 16 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 39.

Sauran wasannin da ke gaban Manchester United a kakar nan:

Premier League ranar Juma'a 16 ga watan Mayu

  • Chelsea da Man Utd

Wasan karshe Europa League ranar Laraba 21 ga watan Mayu

  • Tottenham da Man Utd

Premier League ranar Lahadi 25 ga watan Mayu

  • Man Utd da Aston Villa