Trump ya umarci cire baƙar fata ta farko a shugabannin Babban Bankin Amurka

 Lisa Cook

Asalin hoton, Reuters

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Shugaba Donald Trump ya sanar da aniyarsa ta korar Lisa Cook - Ba'amurkiya tsatson Afirka ta farko da ta rike matsayin gwamna a babban bankin Amurka - a kan zargin almundahana da ba a tabbatar ba a kanta ba.

Mista Trump ya ce cancanta da amanar Ms Cook a wannan matsayi na cikin zargi da tababa a kan zargin aikata abubuwan da suka saba doka a kan batutuwan da suka danganci neman bashin sayen gidaje.

Matakin na ya kasance ne yayin da Trump ke matsa ƙaimi wajen ganin ya samu iko kan yadda ake tafiyar da harkokin bankin.

Daman shugaban na Amurka na takun-saka da shugabancin babban bankin na Amurka a kan kin rage kudin ruwa - abin da shi yake ganin ya dace a yi tuntuni.

Wannan dai wani mataki ne da ba a taba gani ba a tarihin babban bankin na Amurka na shekara 111, a ce wani shugaban kasa na Amurka ya kori mamba a cikin shugabannin babban bankin kasar.

Ita dai Lisa Cook Ba'amurkiya bakar fata - wadda tsohon shugaban kasar Joe Biden ya nada, tana rike da wannan mukami na gwamna ko shugabancin hukumar gudanarwar bankin - daya daga cikin kujeru bakwai na shugabancin bankin.

Ana ganin wannan mataki na Trump zai iya janyo dambarwa ta shari'a a yanzu. Kuma tuni darajar kudin kasar - dala, ta yi kasa a kan batun korar tata.

A makon da ya gabata Shugaba Trump ya bukaci da ta ajiye aikinta a kan zargin cewa ta aikata ba daidai ba dangane da wasu batutuwa biyu da suka danganci sharudan bashin sayen gidaje.

A daren Litinin a wata wasika da shugaban ya sanya a shafinsa na sada zumunta da muhawara - na Truth Social, ya ce akwai cikakkiyar shedar da ta nuna cewa matar ta yi bayanan karya.

Kuma ya bayyana cewa yana aiki ne da ikon da yake da shi na kundin tsarin mulki - kan matakin korar tata.

A wata sanarwa da lauyoyinta suka fitar - Ms Cook ta ce Trump ba shi da ikon cire ta daga wannan mukami, ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da aikinta.

Daman a 'yan watannin nan Shugaban na Amurka na matsa wa babban bankin kasar - wanda ake ganin ba shi da alaka da siyasa a kan ya rage kudin ruwa, abin da bankin ya ki.

Sannan kuma Trump din yana ta barazanar korar shugaban bankin, Jerome Powell.