Southgate zai huta shekara ɗaya kafin ya koma horar da tamaula

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kociyan tawagar Ingila, Gareth Southgate ya ce zai huta shekara ɗaya kafin ya koma horar da tamaula.
Mai shekara 54 ya ajiye aikin kociyan Ingila, bayan da Sifaniya ta yi nasarar lashe Euro 2024 a Jamus a wasan karshe a watan Yuli.
An bai wa Southgate aikin jan ragamar Ingila a 2016, wanda ya kai kasar wasan karshe karo biyu, wato a Euro 2021 da 2024 da yin na huɗu a kofin duniya a Rasha a 2018.
Ana ta alakanta shi da aikin horar da Manchester Unitee, bayan da ake tantama kan makomar Erik ten Hag a Old Trafford.
Southgate ya ce ba zai horar da tawaga ba, idan zai ci gaba da aiki, kuma sai ya natsu kafin ya kullu yarjejeniya da ƙungiya. Ya horar da Middlesbrough tsakanin 2006 zuwa 2009.
Ranar Alhamis, Ingila za ta kara da Girka a Nations League a Wembley, kwana uku tsakani ta kece raini da Finland a Helsinki.
Lee Carsley ne ya maye gurbin Southgate a matakin riƙon ƙwarya, ya kuma yi nasara a wasa biyun da ya ja ragamar tawagar Ingila.






