Waiwaye: Ƴar bautar ƙasar da ke tayar da ƙura a Najeriya da rikicin siyasar jihar Rivers

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Ushie

Asalin hoton, Others

A makon ne ƴan Najeriya suka yi ta tattaunawa dangane da makomar Ushie Uguamaye mai yi wa ƙasa hidima mazauniyar birnin Legas, tun bayan da ta yi zargin fuskantar barazana sakamakon kalamanta da ta yi a shafinta na tiktok inda ta soki gwamnatin Bola Tinubu.

Tuni dai jagororin adawa na Najeriya da kuma ƙungiyoyi masu rajin kare haƙƙin bil'adama suka nemi da hukumar yi wa ƙasa hidima ta NYSC ta tabbatar da cewa babu abin da ya samu Ushie Uguamaye.

Ita dai hukumar ta NYSC ba ta ce uffan ba dangane da zargin barazanar da Ushie Uguamaye ta yi.

Laifukan da ƴanmajalisar dokokin Rivers ke zargin Gwamna Fubara da aikatawa

Fubara

Asalin hoton, X/@SimFubara

A makon ne aka buɗe wani sabon babi a rikicin siyasa da ya turnuƙe a jihar Rivers, bayan da ƴan majalisar dokokin jihar suka zargi gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu da saɓa wa ƙa'idar aiki.

Ƴan majalisa 26 na jihar ta Rivers sun yi waɗannan zarge-zarge ne a wasu takardun koke biyu da suka tura wa shugaban majalisar, Martin Amaewhue.

Sun ce sun ɗauki matakin nasu ne "bisa dogaro da sashe na 188 na kudnin tsarin mulkin Najeriya na 1999", wanda ya tanadi cewa dole ne a samu kashi ɗaya cikin uku na ƴan majalisa su goyi bayan koken sannan kuma a tantance ainahin laifukan.

Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Bola Tinubu

Asalin hoton, X/Bola Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi tare da kuma da naɗa wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar na tsawon wata shida.

Tinubu ya sanar da matakin ne a wani jawabi da ya yi ta kafafen talabijin na ƙasar da yammacin ranar Talata.

A cikin jawabin nasa, Tinubu ya yi nuni da yadda aka rushe ginin majalisar dokokin jihar watanni 18 da suka gabata, wadda aka kasa sake gina ta har zuwa wannan lokaci.

Ladabtar da ɗalibai a makarantu

Ladabi

Asalin hoton, FB/Maikatanga Photography

A makon rundunar ƴansandan jihar Jigawa ta sanar da kama wani malamin makarantar allo bisa zargin duka da ta kai ga kashe wani ɗalibinsa.

Shi dai malamin ya lakaɗa wa ɗalibin duka ne inda ta kai har ya rasa ransa, wani abu da ya sa malamin cire kai da marainan gawar da manufar ɓoye al'amarin ta hanyar nuna cewa matsafa ne suka aikata kisan.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu faya-fayan bidiyo da ke nuna yadda malamai suke ladabtar da ɗalibansu, a kafafen sada zumunta inda wasu suke zagewa iya ƙarfinsu wajen dukan ɗaliban da sunan ladabtar da su.

Yadda motar Ɗangote ta afka kan motoci ta kashe mutum 30 a Abuja

Hatsari

Aƙalla mutum 30 ne suka rasu sakamakon ƙwacewar da wata babbar mota mai ɗauke da kayan siminti ta Ɗangote mai amfani da iskar gas ta yi ta kuma shiga cikin dandazon motoci a Karu da ke kan titin Abuja zuwa Keffi da yammacin ranar Laraba.

Shehu Ɗalhatu wanda shi ne mai kula da yankin Kubo a hukumar kula da ingancin ababan hawa ta Abuja, VIO ya ce "kawo yanzu mutum 30 ne suka rasu sakamakon hatsarin inda wasu kuma ke asibiti suke samun kulawa."

Waɗanda suka shaida faruwar al'amarin sun shaida wa BBC cewa hatsarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Laraba, sun ce wata babbar mota ce ɗauke da kayan siminti da kuma ke gudu na wuce ƙima ta shiga cikin motoci.

Tasirin matakin Dangote na daina sayar da man fetur da naira

NNPC

Asalin hoton, NNPC

A ranar Larabar nan ne matatar man fetur ta Dangote ta sanar da cewa ta dakatar da sayar da man fetur da kuɗin Najeriya wato naira.

Kamfanin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya aika wa dillalan man fetur kuma ya wallafa a shafinsa na X.

Sanarwar matatar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun takun-saƙa tsakaninta da kamfanin mai na Najeriya, NNPCL.

Matatar ta yi ƙarin bayani da cewa an ɗauki matakin ne saboda kaucewa rashin daidaito da ake samu tsakanin ribar da kamfanin ke samu da kuɗin da yake sanya wa masu sayen ɗanyan mai wanda a yanzu galibi da dala suke ciniki.