Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Van Dijk ya bar sansanin Netherland kafin wasa da Bosnia
Virgil van Dijk ya bar sansanin tawagar Netherlands tun kafin wasan Nations League da za ta kara da Bosnia-Herzegovina ranar Talata.
Ƙyaftin ɗin Liverpool ya buga wasan da kasar ta doke Hungary 4-0 ranar Asabar, hakan ya sa ta samu gurbin shiga kwata fainals da za a fara a cikin watan Maris.
Haka kuma koci, Ronald Koeman ya amince Frenkie de Jong ya bar sansanin, wanda ya yi wa tawagar tamaula a karon farko tun bayan wata 13, sakamakon yawan jinya.
Koeman ya ce ya bai wa ƴan wasan damar samun lokacin hutu, domin jikinsu ya koma kan ganiya kamar yadda ya kamata.
Van Dijk ya buga dukkan wasannin Liverpool a bana a Premier League, wanda ya bayar da gudunmuwar da ƙungiyar take ta ɗaya a kan teburi da tazarar maki biyar.
Liverpool karkashin Arne Slot za ta fafata da Southampton ranar Asabar a gasar Premier League.